Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe ‘yan sa-kai 21 a ƙauyen Baure da ke Jihar Katsina.
Sun kai harin ne a ranar Talata, 7 ga watan Janairu, 2025.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma yayin da ‘yan sa-kan ke dawowa daga wata ta’aziyya.
Rundunar ’yansandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce tana ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata wannan aika-aika.
Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar wa jama’a cewa za a gurfanar da masu laifin a gaban shari’a.
Wannan harin ya girgiza al’ummar yankin, yayin da mahukunta ke kira ga jama’a da su kasance masu lura tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin samun zaman lafiya.