Kusan cewa shi farji da a ke magana a kan cututtukansa shi ne wanda Allah ya halitta da wani sinadari na mayen karfe da wata tsoka kuma tana da baki guda biyu hagu da dama. Yayin da sha’awar mace ta motsa sai ta rika motsi dai-dai kuma tana iya yin rauni har ta daina motsi.
Wannan tsoka kamar fulogi ne a jikin mace. Yayin da ta yi mata yawa, sai ta kasa motsi. Daga nan sai sha’awar ‘ya mace ta dauke, domin ita wannan tsoka ita ce ke feso wani ruwa wanda shi ke sauko da wani ruwa da yake samar da jin dadin mu’amalar jima’i kuma yake sa wani zaki tsakanin mace da miji, idan daya daga ma’aurata ya sami matsala, sai ka ga auren ya ki zaman lafiya. Amma idan babu matsala sai ka ga ana zaune lafiya cikin shauki da annashuwa.
- Yadda Mai Haihuwar Fari Za Ta Kula Da Kanta (2)
- An Yi Wa Yara Sama da Miliyan 10 Rijistar Haihuwa Cikin Watanni 3 A Nijeriya
Mafi yawa mata masu ciki suna kamuwa da cututtuka daga wasu kwayoyin halitta dake rike al’aurar mata, saboda gabansu ba ya rabuwa da danshi. Wadannan kwayoyin halittu su ne, bacteria, fungi da sauransu.
Alamomin masu nuni izuwa kamuwar cutar al’aurar mace ya danganta da irin ciwon da abin da ya jawo shi.
Kadan daga ciki: Zafi yayin fitsari
Ciwo daga wajen al’aurarta, canzawar gaba ba kamar yadda ta saba gani ba, Zafi yayin saduwa da miji.
Yadda za ku hada sabulun ko ku saya.
Abubuwan da za ku tanada:
Bagaruwa (Za ku samu a wajen masu magani gargajiya ), Zaitun ( Za ku samu a shagon maganin musulinci, farin miski, Hulba na ruwa. Amma zaplan Zaitun ake hadawa da shi ki duba idan za ki saya amma idan kin rasa zaflan za ki iya sanyan Zaitun.
Yadda za ku hada:
In kin sayo sai ki dauki bagaruwa ki daka tayi laushi ki zuba a roba. Sai ki yayyanka Zaitun din kanana a kan garin Bagaruwa ki nemo miski ki hada tare ki kwava shi da ruwan Hulba, ki kwava sosai ya yi kauri ya damku. Sai ki zuba a roba mai kyau ki rufe.
Idan kwavawa zai baki wahala ki daka a turmi in kin gama wanka sai ki wanke gabanki da shi.
Idan kika kiyaye wadannan babu wani abin da zai hana farjinki dandano ko ni’ima kuma babu ruwan ki da wani matsi idan za ki yi aure. haka za ki shiga gidanki kuma za ki ga yadda za ki gigita mijinki ba tare da kin saka komai a gabanki ba.
Gyaran gaba bayan kin Haihu:
Ina matan da suke haihuwa da yawa ko kuma mata masu matsalar budewa, dole duk macen da ta haihu ta gyara kanta don ita mace yar gyara ce, mu hankalta mata a farka.
Abubuwan da za ku tanada:
Alobera, karo, Zaitun, Kanunfari.
Ki samu Alobera ki samu karo ki jefa kanunfari, ki tafasa ki dinga kama ruwa da shi.
Sannan idan kika samu ganyen Alobera ki matse ruwan ya fito ki dinga wanke gabanki, wanke wa da ruwan dumi, sai kuma ki dinga shafa Zaitun in za ki wurin maigida.