An ambaci Kanem a daya daga cikin manyan dauloli uku a lardin Sudan wanda Ya’kubi yayi a shekarar 872.Ya yi bayani kan daular “Zaghāwa wanda ya zauna a wani wuri da ake kira Kānim”, wanda ya kunshi wasu jihohin vassal masu yawa.
“Wuraren da suke kwana a bukkoki ne wadanda aka yi da ciyawa ba kuma su da wasu Birane.” Suna zama da rayuwa ce kamar ta Fulani masu kiwo, yadda suke hakan ya basu dama suka zama ja gaba a vangaren soja. A karni na 10, al-Muhallabi ya ambaci Birane biyu a wata daula,daya daga cii sunanta Manan.
- An Kashe ’Yan Ta’adda 34 Da Sojoji 6 A Harin Borno – Shalkwatar Tsaro
- Tinubu Ya bayar Da Umarnin Bincike Kan Harin Da Boko Haram Ta Kai Wa Sansanin Sojoji A Borno
Sarkinsu an dauke shi wani babban al’amari, an yarda da shi ke bada ‘’rayuwa da mutuwa’’ “mai bada ciwo da lafiya”. Dukiya ana maganar ta da dabbobi, Tumaki,Shanu, Rakumma da kuma Dawakai.
Daga Al- Bakri a karni na 11 har zuwa abinda yayi gaba, ana kiran masarautar da sunan Kanem.A karni na 12 Muhammad al- Idris ya ambaci Mānān a matsayin “wani karamin Birni wanda baya da masana’anta ko kuma harkar data shafi Kasuwanci”.Ibn Sa’id al Maghribi ya kira Mānān a matsayiin hedikwatar Sarakunan Kanem a karni na 13 da kuma Kanem take da wani jarumin Sarki’.
Daular Saifawa shekarata (850 zuwa1846)
Kanuri da suke musulmai sun samu damar shiga Kanem ne daga mutanen Zaghawa wadanda masu kiwo ne a karni na 9 lokacin da aka samu matsalar . Wani mashahurin Kanuri ya bayyana cewa Sayf ibn Dhi Yazan shi ne ya samo daular Sayfawa. Sabuwar daular ita ce take rike da lamarin kasuwanci na Zaghawa a tsakiyar Sahara tare da Bilma da sauran wuraren da ake hakar gishiri.Sai dai duk da haka maganar kasuwancin shi ne lamarin Bayi. Kabilun da suke Kudu da tafkin Chadi an kai masu hari ko mamaya a matsayin Kafirun,daga can sai aka kai su zuwa Zawila a cikin Fezzan,inda ake bayar da mutane Bayi a bada Dokuna da makamai.A ko wace shekara ana samun karuwar yawan Bayin da aka yi ciniki daga 1000 a karni na 7 zuwa 5000 a karni na 15.
Kamar yadda Richmond Palmer yace abin na al’ada ne a samu Mai yana zaune “Mai yana zaune ko ya zauna kan wani abinda ake kira da suna fanadir, dagil, ko tatatuna.Wani abin zama ne aka yi da fatar dabbar daji.”
Mai Hummay ya fara mulkin sa ne a shekarar 1075, inda ya kulla kawance da Kay, Toubou, Dabir,da Magumi.Shi ne Sarki musulmi na farko na daular Kanem, bayan da aka sa shi ya karbi shahada daga wurin Malamin shi Muhammad Man.Sai suka ci gaba da kasancewa tare a matsayin masu kiwo har zuwa karni na 11, lokacin da suka mai da hedikwatar zuwa Nijmi.
Humai shi ya gaji Dunama na 1 daga shekarar (1098 zuwa1151),ya yi aikin Hajji sau uku kafin ya samu matsalar data shafi ruwa a Aidab.A wancan lokacin, sojoji sun hada da 100,000 wadanda suke kan Dawakai da kuma sojoji zalla 120,000.