Shugaban tsangayar nazarin kimiyyar halittun fili da na voye da har hada magunguna na jami’ar Bayero da ke Jihar Kano, Farfesa Tijjani Hassan Darma, ya bayyana cewa yanzu haka jami’ar ta gano cewa a hoton yatsa za a iya gane mai cutar daji.
Ya ce ta hanyar daukar hoton mace za a iya gano tana da kansa ko babu, ba tare da wani vata lokaci ba ko wani dogon gwaje-gwaje, a karon farko a tsakanin jami’o’in duniya, musamman da aka lura mata sun fi maza kamuwa da cutar kansa (Daji).
- Da Ɗumi-ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 80 A Katsina
- Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa
A cewarsa, jami’ar ta gano wannan lamarin ne ta hanyar saka gasa a tsakanin daliban kimiyya, inda wata dalibar jami’ar a cibiyar ASPAK da ke karkashihn Farfesa Halima Galadanchi, wannan daliba ta gano wannan fasaha bayan gasar da aka saka musu kuma ta samu kyaututtuka.
Farfesa T.H Darma ya bayyana hakan ne a lokacin babban taron da tsangayar ta shirya tare da hadan gwiwar kwalejoji uku a karo na bakwai a jami’ar.
Har ila yau, Farfesa Darma ya ce sassa uku da suka hada da sashin nazarin kimiyyar rayuwar halittu da sashin kimiyyar lissafi da abubuwan da ido ke iya gani har ma da wanda baya gani da kuma sashin harhada magunguna suka shirya baje kolin ilimi domi yin nazarin bincike da zai amfanar da masana da jami’o’i da kuma sauran al’umma.