Kasar Sin ta jaddada adawarta da takunkumin da Amurka ta kakaba a kan shigo da kayayyakin fasahar kirkirarriyar basira ta AI cikin kasarta daga waje, inda ta ce tabbas za ta dauki matakai na kare halasci da ‘yancin kasuwanci na kamfanonin Sin, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana yayin gudanar da taron manema labarai na yau da kullum a yau a birnin Beijing.
Da yake magana game da alakar Sin da Amurka, Guo Jiakun ya ce duk da an samu kwan-gaba-kwan-baya a dangantakar kasashen biyu cikin shekaru hudun da suka gabata, amma kuma idan aka duba lamarin baki daya, an samu jituwa.
Guo ya kuma ayyana cewa, a ko wane irin sauyi da za a samu na huldar kasashen duniya, kasar Sin za ta ci gaba da zama rundunar wanzar da zaman lafiya, da kawo ci gaba, da samun bunkasa da nuna hali nagari tare da aiki da sauran kasashen duniya wajen tabbatar da kwanciyar hankali da daukaka ci gaba na bai-daya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)