Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci takwaransa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi, da ya gargadi magoya bayansa da su daina yada karairayi da zage-zage da bata masa suna.
Tinubu, a wata sanarwa da Daraktan yada labaransa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, ya gargadi Obi da ya kame hannu da bakin magoya bayansa kuma ya bukace su da su bar zaben 2023 dake gabatowa a yi shi cikin kwanciyar hankali a Nijeriya.
Ya ce tsarin zaben Nijeriya zai inganta idan yakin neman zabe ya tsaya kan al’amuran da suka shafi shugabanci na gari da zai fitar da miliyoyin ‘yan Nijeriya daga kangin talauci maimakon a mamaye ‘yan Kasar da zancen karya da bata suna da wadanda ba sa yi wa kasar fatan alheri ke yi.
Mista Onanuga ya nusar da bukatar jan hankalin dan takarar Labour party ne biyo bayan wani rahoton karya da aka fitar kuma aka gano asalin rahoton cewa daga magoya bayan Peter Obi yake.
Rahoton yayi ikirarin cewa shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya rubuta wa Tinubu wasika, inda ya bukaci Tinubu ya marawa Peter Obi baya, Shi kuma ya kula da lafiyar sa.
Hakan yasa, Shugaban kasar Ghana ta shafinsa na Twitter ya yi watsi da wasikar karyar inda ya bayyana ta a matsayin wata barna da gangan da nufin yaudarar jama’a.