Kamfanin samar da wutar lantarki na kasa (TCN) ya koka kan yadda ake samun karuwar barnata turakun wutar lantarki a fadin Nijeriya.
TCN ya ce, fiye da turaku 18 ne aka lalata tsakanin 9 zuwa 14 ga Janairu, 2025, a fadin jihar Rivers, Abia, da Kano.
- TikTok Ya Dawo Aiki A Amurka Bayan Matakin Da Trump Ya Ɗauka
- Tashar Tekun Ningbo-Zhoushan Ta Sin Ta Sake Zama Kan Gaba A Duniya A 2024
Karuwar na matukar bayar da babbar barazana ga fannin dorewar samar da wutar lantarki a kamfanin. Sai dai, mun karfafa matakan tsaro, da kara sintiri a jerin layukan turakun, muna kuma hada kai da jami’an tsaro.
Amma duk da haka, muna buƙatar cikakken goyon bayan kowane ɗan Nijeriya, musamman al’ummomin da turakun wutar lantarkin ke cikinsu. Dole ne kowa ya fahimci cewa, wutar lantarki na daya daga cikin muhimman kadarorin kasarmu ta gama gari kuma tana da muhimmanci don ci gaban tattalin arzikinmu.
Masu barna da masu sayen kayan sata suna yiwa al’umma da kasarsu zagon kasa ne. Dole ne mu hada kai kuma mu tashi tsaye wajen tabbatar da bunkasar bangaren samar da wutar lantarki a kasar, wanda ke da matukar muhimmanci ga ci gaban kasarmu.