A yau Litinin, shugaban kasar Sin, kuma sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya gabatar da sakon gaisuwa, na murnar zagayowar bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ga daukacin ’ya’yan jam’iyyun siyasar kasar da ba ’yan Jam’iyyar kwaminis ba, da na gamayyar kungiyoyin masana’antu da cinikayya na kasar, da jami’ai wadanda ba su da wata jam’iyya, da sauran mambobin rukunoni masu ingiza manufofin JKS, gabanin bikin bazarar dake tafe.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar, ya aike da sakon gaisuwar ne, yayin da ya halarci gangamin bikin shekara-shekara tare da ’ya’yan jam’iyyun siyasar kasar da ba ’yan Jam’iyyar kwaminis ba, wanda ya gudana a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing.
- Sin Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Ga Wani Mutum Kan Kashe Mutane 35 A Tukin Ganganci
- Mun Shirya Yin Gwanjon Motoci 850 Da MuKa Ƙwace – EFCC
Yayin taron, Xi ya ce Sin za ta aiwatar da karin managartan matakai, da manufofin inganta tattalin arziki, da mayar da hankali ga ci gaba mai inganci, da ingiza matakan dogaro da kai, da karfafa kimiyya da fasaha, don wanzar da saurin bunkasar zamantakewa da tattalin arzikin kasa a shekarar nan ta 2025.
Xi, ya yi kira ga mambobin jam’iyyun da ba na JKS ba, da na ACFIC, da jami’ai wadanda ba su da wata jam’iyya, da su mayar da hankali ga ayyukan tsakiya, da aiwatar da abubuwan da za su ingiza moriyar kasar, da amfani da fifikon karfi na jawo goyon baya daga sassa daban daban, da gina tsarin cimma matsaya daya, da tattaro basira da karfin raya kasa. (Saminu Alhassan)