”Idan zamani ya dinka riga, ya kamata a saka.” Wannan magana ta nuna hikimar Hausawa ta kokarin tafiya tare da zamani a ko yaushe. Sa’an nan yadda kasar Najeriya ta shiga tsarin BRICS+ a matsayin abokiyar hulda a kwanan nan, shi ma ya nuna hikimar tafiya tare da yanayin zamani sosai.
Ko mene ne yanayin zamani da Najeriya ta tafi da shi? Shi ne haskakawar tauraron kasashe masu tasowa, ko kuma “Global South” a bakin Turawa, a duniya.
- Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu
- Ba Ma Cikin Waɗanda Suka Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Katsina
Mun san rikicin hada-hadar kudi da ya abku a shekarar 2008 ya sa dimbin kasashe masu sukuni fuskantar matsalar koma bayan tattalin arzikinsu. Tun daga lokacin, wasu kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa cikin sauri, ciki har da kasar Sin, sannu a hankali suka fara zama wadanda ke samar da mafi yawan karuwar tattalin arzikin duniya. Daga bisani, wadannan kasashe sun yi amfani da tsarin hadin gwiwa na BRICS wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a duniya, da taimakon sauran kasashe masu tasowa wajen zamanantarwa, ta hanyar hadin gwiwa a fannonin cinikayya da masana’antu. A lokacin da ake aiwatar da wannan mataki, kasashe masu tasowa sun fara taka muhimmiyar rawa a fannin kulawa da al’amuran duniya, inda suke kokarin yin garambawul da zai tabbatar da adalci, da daidaituwa, gami da wakiltar mafi yawan kasashe.
Yanzu kasar Najeriya ita ma ta shiga tsarin BRICS+, kuma hakan zai kara karfin tsarin hadin gwiwa na BRICS+, ganin yadda yawan al’ummarsa zai kai kaso 54.6% na daukacin al’ummar duniya, kana GDPnsa zai kai kaso 42.2% na adadin na duniya. Hakan zai sa kasashen BRICS da abokan huldarsu samun damar karfafa wa kasashe masu tasowa ikon fada-a-ji, da inganta wakilcinsu a hukumomin duniya, gami da sanya tsarin hada-hadar kudi na duniya ya dace da yanayin ci gaban kasashen da tattalin arzikinsu ke kan hanyar tasowa.
Sa’an nan a nata bangaren, Najeriya za ta samu alfanu a fannoni daban daban, ta hanyar zama abokiyar huldar kasashen BRICS, wadanda a kalla suka kunshi wadannan bangarori: Wato na farko, bisa tsarin gudanar da ciniki da kudin kashin kai na ko wace kasa da kasashen BRICS ke kokarin yayatawa, Najeriya za ta iya aiwatar da karin cinikin waje da kudinta na Naira, don rage dogaro kan dalar Amurka. Ta haka, kasar za ta samu damar sasanta matsalar karancin kudin musaya, wadda kan haddasa matsalar tafiyar hawainiya ga ci gaban tattalin arziki a kasar.
Na biyu, nan gaba Najeriya tana da damar samun bashi daga bankin raya kasa na NDB, da tsarin samar da kudi cikin gaggawa na CRA, duk a karkashin tsarin BRICS, don tallafa wa ayyukanta na gina kayayyakin more rayuwa, da dai sauransu.
Na uku, a matsayinta na babbar kasa mai dimbin al’umma da karfin tattalin arizki ta nahiyar Afirka, Najeriya na neman zama mai fada-a-ji a Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomi na duniya. To, kasar tana da damar cika burinta a wannan fanni, bisa goyon bayan da za ta iya samu daga tsarin BRICS+.
Na hudu, idan an yi nazari tare da hangen nesa, to, za a ga yadda wasu abubuwan da tsarin BRICS+ ya kunsa, irinsu kasancewar mabambantan al’adu tare cikin daidaito, da cudanya tsakaninsu don neman koyi da juna, za su taimaki Najeriya, a kokarinta na lalubo hanyar raya kai, wadda za ta dace da ainihin yanayin da kasar ke ciki. Wannan shi ne dalilin da ya sa ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta furta cewa, zama abokiyar huldar kasashen BRICS “wani gwaji ne mafi kyau a kokarin kasar na tabbatar da tsare-tsaren raya kasa na kashin kanta”. (Bello Wang)