A bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, an kai waɗanda suka jikkata a haɗarin fashewar tankar man fetur a Suleja zuwa manyan asibitoci don su samu kulawa ta musamman.
A cikin wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ya fitar, ta ce an kwantar da mutane 20 a Asibitin Ƙwararru na Gwagwalada da ke Abuja, yayin da aka kai wasu mutum biyu zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Jabi, Abuja.
- Tinubu Ya Himmatu Wajen Kammala Titin Abuja Zuwa Kano Cikin Watanni 14 – Minista
- Tinubu Ya Himmatu Wajen Kammala Titin Abuja Zuwa Kano Cikin Watanni 14 – Minista
Sanarwar ta ƙara da cewa duk wanda aka tura an raka shi da mai jinya da kuma iyalin sa domin tabbatar da ingantacciyar kulawa yayin canja wurin.
Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana godiyar ta ga Gwamnatin Tarayya kan saurin ɗaukar mataki da ingantaccen martani da aka nuna wajen magance wannan mummunan lamari.
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta tabbatar wa da jama’a cewa za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da bayar da bayanai a kai a kai.