Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, ta kafar bidiyo da maraicen yau Talata 21 ga wata, a babban dakin taron alumma dake Beijing.
Shugaba Xi ya ce, a shekara ta 2024, kasashe Sin da Rasha sun zurfafa hadin-gwiwa da muamala a karkashin tsarin Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar hadin-gwiwa ta Shanghai wato SCO, da kuma kungiyar kasashen BRICS, inda suka bayar da gudummawa ga yin gyare-gyare gami da raya tsarin daidaita harkokin duniya.
- Tsakanin Nijeriya Da BRICS+: Idan Zamani Ya Dinka Riga…
- Samar Wa Nijeriya Sabon Kundin Tsarin Mulki Zai Magance Matsaloli – Moghalu
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, bana ake cika shekaru 80, da jamaar kasar Sin suka samu galaba kan yakin kin maharan Japan, kana tsohuwar tarayyar Soviet ta samu nasara kan yakin kare kasa, kuma aka samu nasara kan yakin kin fascism a duk duniya. Kaza lika, lokaci ne na cika shekaru 80 da kafa Majalisar Dinkin Duniya. Ya ce ya dace kasashen Sin da Rasha su yi amfani da wannan dama, don kiyaye tsarin sassan kasa da kasa mai jigon MDD, da nasarorin da aka cimma daga yakin duniya na biyu, da taimakawa kasa da kasa su mutunta kaidoji da manufofin kundin tsarin mulkin MDD, da tsayawa ga muhimman kaidojin dangantakar kasa da kasa, da aiwatar da raayin cudanyar bangarori daban-daban a zahiri.
Shi kuwa shugaba Putin cewa yayi, yana farin cikin ganin ci gaban hadin-gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da kasuwanci da makamashi. Kasar Rasha na goyon-bayan cewa, Taiwan, yanki ne da ba zaa iya balle shi daga kasar Sin ba, kuma tana adawa da duk wani yunkuri na ware Taiwan daga kasar Sin. Ya ce Rasha na fatan karfafa hadin-gwiwa tare da kasar Sin a harkokin kasa da kasa, don haifar da da-mai-ido ga shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba a duniya. (Murtala Zhang)