Biranen kasar Sin na gudanar da gyare-gyare na ci gaban zamani a bangaren kyautata jin dadin baki masu kawo ziyara ko kuma yada zango. Inda hakan ke haifar da kyakkyawan sakamako daga irin tsokacin da baki ke yi kan sabbin tsare-tsaren da suka gani a biranen.
Wasu ‘yan uwa su biyu daga Poland da suka kawo ziyarar kwanaki hudu a birnin Beijing kwanan baya, sun bayyana cewa, kasar Sin ta burge su sosai, bisa yadda suka ga an ci gaba da raya manyan biranen kasar tare da saukaka mu’amalar biyan bukatun masu yawon bude ido na kasashen waje.
- Kasar Sin Ta Mallaki Tashoshin Sadarwar 5G Miliyan 4.25
- Borrusia Dortmund Ta Sallami Kocinta, Nuri Sahin
Dagmara Paszkowska, wacce ta ziyarci kasar Sin tare da dan uwanta Norbert ta ce, “Mun lura za mu iya biyan kudin hidindimu ko abubuwan da muka saya ta hanyar amfani da tsabar kudi, ko kati, ko kuma ta hanyar tambarin QR, kana mun yi mamakin cewa ana ma iya amfani da hanyar tantance fuska wajen biyan kudi.”
A wani bangare na sabon tsarin biyan kudi da tafiye-tafiye da aka kaddamar a ranar 1 ga Janairun nan don saukaka mu’amaloli ga baki, an samar da wuraren tuntuba don neman biyan bukata ta kusurwowin da bakin za su yi kacibis da su da zarar sun iso manyan filayen jiragen sama guda biyu na Beijing, wato na Beijing Capital da na Beijing Daxing.
Kaddamar da wadannan wurare da birnin Beijing ya yi a manyan tasoshinsa na jiragen sama ta zo a kan gaba, a daidai da lokacin da ake samun karuwar baki daga kasashen waje sakamakon fadada manufofin kasar Sin na shigowa ba tare da biza ba ga matafiya daga kasashe 54, da kuma damar shiga kai-tsaye ga baki masu fasfo daga kasashe 38 da ke bukatar gajeren zama a kasar.
A halin yanzu, kusan a kullum, ana samun baki ‘yan kasashen waje 252 de ke shiga birnin Beijing tare da takardar izinin shiga ta wucin-gadi ta sa’o’i 240 wacce aka kara mata wa’adi daga sa’o’i 144, kamar yadda mataimakin shugaban sashen musayar waje da hadin gwiwa na ofishin al’adu da yawon bude ido na birnin Beijing, Wang Hongyan, ya tabbatar a wani taron manema labarai.
A shekarar 2024, birnin Beijing ya sami ziyarce-ziyarce miliyan 3.94, wadanda suka karu da kashi 186.8 cikin dari a mizanin shekara-shekara, inda hakan ya kara yawan kudin shiga na yawon bude ido na birnin da kashi 151.7 cikin dari, watau zuwa dala biliyan 4.91, kuma mahukuntan da abin ya shafa sun lashi takobin kara kyautata jin dadin baki masu ziyara ta hanyar inganta tsare-tsaren yawon bude ido, masaukai da sayayya da hanyoyin biyan kudi masu gamsarwa.
Tsarin amfani da katin komai-da-ruwanka na “Beijing Pass” na daga cikin abubuwan da ke saukaka mu’amalar baki a birnin ta yadda wadanda suka saye shi ba kawai za su iya amfani da shi wajen biyan kudin sufuri a cikin birane 300 na kasar Sin ba ne, har ma za su iya shiga wasu kebabbun wuraren kasuwanci, da cibiyoyin tarihi da al’adu da yawon bude ido. An bayar da wannan kati a kalla 39,000 ga baki masu ziyara daga lokacin da aka kaddamar da shi a watan Yulin bara.
Haka nan, domin bai wa baki damar sanin tarihi da al’adun Sinawa a Beijing, a ranar 27 ga Disamban da ya gabata, birnin ya yi sabon albishir ta hanyar kaddamar da tsarin kai bakin da suka yada zango a cikinsa ziyara ta rabin yini a wasu muhimman wurare kyauta. Ana gudanar da wannan tsari sau biyu a yini, da safe da kuma maraice.
Sauran biranen kasar Sin kamar Shanghai su ma suna ci gaba da janyo hankulan dubban masu kawo ziyara saboda manufar shigowa ba tare da biza ba. A watannin baya-bayan nan, alal misali, ana samun karuwar maziyartan Koriya ta Kudu dake tururuwa zuwa birnin Shanghai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)