Ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta ce adadin tashoshin samar da tsarin sadarwa na 5G dake akwai a kasar ya kai miliyan 4.25, inda adadin masu amfani da kafar sadarwar intanet ta wayar salula mai saurin gigabit, ya zarce miliyan 200.
A cewar ma’aikatar, an kafa sama da kamfanoni 4,000 na samar da sadarwar 5G a fadin kasar.
- An Sallami Saif Ali Khan Daga Asibiti Bayan Harin Da Aka Kai Masa
- Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Bai Wa Kamfanin Bogi Kwangilar Aikin Hanyar Abuja-Kano
Ta kara da cewa, adadin masu amfani da wayoyin salula masu tsarin sadarwar 5G ya zarce biliyan 1, inda tsarin ya mamaye adadin al’umma da ta kai sama da kaso 71, kuma matsakaicin yawan sadarwar intanet na tafi da gidanka wato data da suke amfani da shi a ko wane wata, ya kai gigabyte 19.
A cewar ma’aikatar, amfani da kayayyaki masu fasahohi na zamani na bunkasa kasar, lamarin da ya sa kudin hidimomin fasahohin da ake amfani da su ya zarce yuan tiriliyan 6, kwatankwacin dala biliyan 833. (Fa’iza Mustapha)