Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta jagoranci taron manema labarai a yau Laraba 22 ga wata, inda ta amsa tambayar da aka yi mata, game da shirin shugaban Amurka Donald Trump na kara buga harajin kwastam kan hajojin da kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurka, tana mai cewa, kasar Sin na ganin cewa, babu wanda zai samu galaba a yakin cinikayya ko yakin harajin kwastam, kana, kasar Sin tana tsayawa kan kiyaye muradun kanta.
Kaza lika, game da matakin Trump na kara buga harajin kwastam har kaso 100 bisa dari kan kasashen BRICS, Mao Ning ta ce, a matsayin kasuwa dake tasowa, kana muhimmin dandalin hadin-gwiwar kasashe masu tasowa, tsarin kasashen BRICS na kira da a bude wa juna kofofi, da yin hakuri, da inganta hadin-gwiwa don cimma moriya tare, maimakon yin fito-na-fito da juna, kuma babban makasudin BRICS shi ne samar da ci gaba da bunkasuwa tare.
Kasar Sin na fatan ci gaba da kokari tare da abokan tafiya na BRICS, don zurfafa hadin-gwiwa a fannoni daban-daban, da kara bayar da gudummawa ga habakar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. (Murtala Zhang)