Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), karkashin atisayen Fansar Yamma, ta halaka ƴan ta’adda da dama tare da lalata sansanin ajiyar makamansu a Alawa, ƙaramar hukumar Shiroro, Jihar Neja.
Mai magana da yawun NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya ce an kai wannan farmaki a ranar 21 ga Janairu, 2025, bayan samun sahihan bayanan sirri da hotunan binciken sararin samaniya da ya tabbatar da yawaitar ƴan ta’adda a cikin dajin. Ya ce ƙungiyar tana da alaƙa da hare-haren bama-bamai guda biyu da suka faru a ranar 19 ga Disamba, 2024, a Bassa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
- NAFDAC Ta Rufe Babban Kantin ‘Yan China A Abuja Saboda Saɓa Dokoki
- Duk Mai Burin Aurena, Ya Fara Sani Na Don Gudun Shiga Matsala – Nafisa Abdullahi
Akinboyewa ya ƙara da cewa NAF ta ƙaddamar da farmaki mai suna “ƘONAN DAJI” na tsawon kwanaki uku, tare da aika jiragen yaki domin kai hari kan wuraren ƴan ta’addan. Wuraren da aka kai hari sun lalace sosai bayan harba roka wanda ya tayar da fashe-fashe masu yawa.
Ya bayyana cewa NAF, tare da haɗin gwuiwar Sojojin ƙasa, za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa ga al’ummomin da ke cikin Jihar Neja da kewaye.