Wata babban kotu a jihar Akwa Ibom ta daure wasu mutum uku bisa nau’ikan sojan gona daban-daban domin damfara da sunan hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangoginta (ICPC).
Daga cikin wadanda kotun ta daure sun hada da wani babban malamin addinin kirista, Rabaran Nobert Rampa, Mai shekara 53 a duniya dan asalin Ekpene Ukim da ke karamar hukumar Uruan, bisa kamasa da laifin damfarar mutane da karyar cewa shi babban jami’i ne a wadannan hukumomin biyu na EFCC da ICPC.
Sauran sun hada da Gabriel Udo mai shekara 34 a duniya wanda ke sana’ar aski daga kauyen Mbiafum Ikot Abasi a karamar hukumar Ini tare da Patrick Essien, 52, da ya fito daga Uruan.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Archibong Archibong ya kama wadanda ake zargin da damfara da sojan gona don haka ya daure su a karkashin sashin s 552, 112 da 495 na final kod Cap 38, Vol 2, na dokokin jihar Akwa Ibom ta shekarar 2000.
A hukuncinsa na tsawon sama da awa biyu, Archibong ya ce bisa tulin shaidu da hujjojin da aka gabatar wa kotun, ya amince da cewa masu shigar da kara sun gamsar da kotun kan wadanda suke kara bisa tsarin doka.
Alkalin kotun ya daure wanda ake zargi na farko da na biyu zan shekara 25 a gidan yari, yayin da wanda ake zargi na uku ya samu hukuncin za a gidan yari na tsawon shekara 3.