Babban Lauyan Jihar Kano, Haruna Dederi, ya janye dukkanin ƙararrakin da aka shigar kan masu zanga-zangar #EndBadGovernance a jihar.
Wannan mataki ya biyo bayan wata takarda da wata ƙungiya mai zaman kanta Citizens’ Gavel, ta gabatar a watan Nuwamban 2024.
- Sulhu da ‘Yan Bindiga Ya Fi Zubar Da Jinin Ɗan Adam A Kaduna – Uba Sani
- Al-Hilal Ta Raba Gari Da Neymar
A cikin takardar ta roƙi Babban Lauyan da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi don janye ƙararrakin.
An kama masu zanga-zangar ne yayin zanga-zangar yunwa a watan Agusta 2024.
An tuhume su da laifuka da suka shafi haɗa baki da kuma tayar da hankali da cin amanar ƙasa.
Citizens’ Gavel ta bai wa waɗanda ake tuhuma tallafi ta hanyar taimaka musu a shari’a domin kare haƙƙinsu.
A wata sanarwa, ƙungiyar ta yaba wa matakin Babban Lauyan, inda ta ce wannan adalci da kuma kare ‘yancin ‘yan ƙasa na yin zanga-zanga cikin lumana ba tare da tsangwama ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp