Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ƙaddamar da aikin shimfiɗa titin Koko zuwa Dabai da ke Ƙaramar Hukumar Zuru, wanda zai ci Naira biliyan 64.
Aikin zai gudana ne ƙarƙashin kamfanoni uku, kuma ana sa ran za a kammala shi cikin watanni 18.
- Sojoji Sun Ƙwato Makamai, Sun Ci Gaba Da Neman Bello Turji A Zamfara
- Wa’adin Ficewar Nijar, Mali Da Burkina Faso Daga ECOWAS Ya Cika Yau
Hanyar, wacce ta kai tsawon kilomita 87, ta kasance mallakar gwamnatin tarayya.
Sai dai saboda jinkirin aiki, an soke kwangilar baya, kuma hukumomin tarayya sun bayar da dama ga gwamnatin Kebbi ta ɗauki nauyin aikin, tare da alƙawarin mayar mata da kuɗaɗen da ta kashe bayan an kammala aikin.
Gwamna Nasir ya bayyana cewa, ko da gwamnatin tarayya ta biya ko ba ta biya ba, gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin aikin, ganin yadda titin ke da matuƙar muhimmanci ga al’ummar jihar da ma Nijeriya baki ɗaya.
Ya gargaɗi kamfanonin da suka samu kwangilar da su tabbatar da ingantaccen aiki, tare da jaddada cewa za a hukunta duk wanda ya kasa cika sharuɗan aikin.
Sannan, ya buƙaci direbobin manyan motoci da su guji lodin da ya fi ƙarfin titin domin kare lafiyar matafiya da rage hatsari.
Don haka, gwamnati za ta kafa kwamiti don tabbatar da bin doka da oda a kan titin.
Kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Abdullahi Umar Faruk, ya bayyana cewa kashi 40 na kuɗin aikin an riga an biya.
Ya ce an biya kamfanonin kuɗin kamar haka:
- Kamfanin ZBBC zai shimfiɗa titin daga Dabai zuwa Mahuta (kilomita 25) a kan Naira biliyan 18.
- Kamfanin Habib Engineering LTD zai yi aikin daga Mahuta zuwa Marafa (kilomita 25) a kan Naira biliyan 18.
- Kamfanin GNIC zai yi aikin daga Koko zuwa Marafa (kilomita 37) a kan Naira biliyan 27.
Baya ga titin Koko – Zuru, Gwamna Idris ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta inganta babban asibitin Zuru domin ya zama cibiyar ƙwararru.
Haka nan, a yayin ziyarar godiya da ya kai ƙananan hukumomin Fakai, Sakaba, Danko Wasagu, da Zuru, ya kuma ƙaddamar da wata hanyar karkara mai tsawon kilomita 11 daga Koko zuwa garin Kangin Korama, wanda aikin zai ci Naira biliyan 1.3.