Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin Omoyele Sowore, shugaban rajin #RevolutionNow, kan kuɗi na Naira miliyan 10.
Kotun ta ce dole ne ya kawo wanda zai tsaya masa wanda ke da kadarori da darajarsu ta kai kimanin adadin kuɗin belin.
- Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje
- Isra’ila Ta Dakatar da Sakin Fursunonin Falasɗinawa Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Wanda zai tsaya masa dole ne ya gabatar da takardun kadara da hoton fasfo ɗinsa ga rajistan kotun.
Sowore kuma ya wajaba ya miƙa fasfo ga kotu.
Alƙalin kotun ya bai wa Sowore awanni 24 don ya cika sharuɗan belin, idan ba haka ba, zai ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan sanda har sai ya cika sharuɗan.
Sowore, wanda ya taɓa tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa, na fuskantar tuhume-tuhume guda 17 daga rundunar ‘yansanda, ciki har da laifi a kafafen sada zumunta da kuma kiran Shugaban ‘Yansanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, da “IGP na ƙarya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp