…ci gaba daga makon jiya
Wuraren da jami’in ilimi zai iya yin aiki
Jami’in ilimi shi kwarare ne wanda shi ke da alhakin shiryawa, aiwatarwa,da kuma lura da lura da lalle ana yin lamurran kamar yadda manufofin da tsare- tsaren ilimin suka dace a tafiyar da su.Suna iya yin aiki ta dukkan kowane yanayi,ko wurare da suka hada da makarantu, hukumoin gwamnati da kuma kamfanoi masu zaman kan su.Hanyar samun aikin shi tana farawa ne da mallakar takradar shedar digiri a bangaren ilimi ko kimiyyar zamantakewa, ko kuma wani darasi da yake da alka da aikin da za ayi.Bayan kammala karatun digirin su na farko suna iya yin digiri na biyu duk a bangaren ilmin ko kuma wani sashe da yake na musamman, bayan sun kammala digirinsu na fako, suna iya yin na biyu ta bangaren ilimi ko kuma wani bangare na musamman kamar, shugabancin ilimi, bunkasa darussan ilimi,ko yadda tsarin yake. Duk da haka akwai bukatar jami’an ilimi. Jami’an ilimi akwai bukatar su mallaki takardar shedar koyarwa ko kuma lasin,wannan kuma ya danganta ne kan irin gudunmawar da suke badawa da kuma inda ya dace su tsaya.
Da Zarar sun kammala karatunsu suka mallaki dukkan matakan ilimin da suka kamata su samu, jami’an ilimi suna iya suna iya samun ko mallakar matakin da ake bukatar su kai kamar na kwararru kan abubuwan da za a koyar, ko jagoran tafiyar da tsari, ko kuma mai koyar da Malami.Wadannan a yadda aka sani sun hada da aiki da Malamai da jami’an mulki domin samar da tsare- tsaren ilimi da gabatar da su wadanda suka yi daidai da muradan/ manufofi hukumomin.Ya yin da su jami’an ilimi suke samun kwarewa da hakan za isa su zama sun gane aikin nas kamar yadda kowa yake so,da hakan suna iya samun karin girma zuwa wasu mukamai kamar darektan ilimi, ko kuma babban jami’in Koyarwa.
Wadannan ayyukan sun hada lura da yadda ake inganta da aiwatar tsare- tsare da manufofin ilimi da sassa da kuma hukumomi.Matsayin jami’an ilimi a mukamin su sune ke da alhakin kula da yadda ake tafiyar kasafiun kudi, hadin kai da abokan hulda yadda za su rika kokarin samun tsare- tsaren ilimi da kuma kudaden taimako ko daukar nauyi.Bugu da kari akwai ilimin da aka tsara yadda za a koyar da shi, jami’in ilimi da yake da kwarewa sun ,mallaki dabaru masu yawa da wasu karin abubuwan da ake bukata daga wurinsu.Wadannan sun hada da saniun makamar yadda za ayi hulda da mutane da kuma yawon yadda za a nakalci yadda lamurra suke, da kuma sha’awa da nuna son koda wane lokacin ana bukatar koyon wani sabon abu.
Hakanan ma akwai su yi aiki duk irin halin da suka samu kansu, su san yadda lamurran ilimi za su tafi kamar yadda ya dace.Ko mai dai menene hanyoyin ko wuraren da jami’an ilimi za su iya yin aiki suna da yawa da kuma yadda za su samu ci gaba ta kowane hali suka tsinci kansu.Ko dai suna aiki a makarantar lardi ko hukumar da ke karkashin gwamnati,ko hukumar wadda ita babu ruwanta da riba, jami’an ilimi suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da duk wadanda suke son ilimi ana koya masu ta nagartattar hanyar da za ta kasance da hanyoyin karuwa.
Irin ayyukan da jami’in ilimi zai iya yi
Jami’inilimi kwararre ne wanda kuma har ila yau alhakin tafiyar harkokin,manufofin,da tsare- tsaren ilimi suka rataya a wuyansa, wannan ma har ya hada da yadda za a cimma nasarar yin hakan.Suna yin ayyuka a hukumomi daban- daban da suka hada da makarantu, kwalejoji, jami’oi, da kuma hukumomin gwamnati.Babban aikin su shi ne samar da kuma gabatar da tsare- tsare wadanda za su taimakawa ci gaban lamurran ilimi.Hakanan ma suna aiki kafada- kafada da Malamai, ‘yan makaranta, Iyaye, da sauran masu fada aji, domin tabbatar da cewar na tafiyar da lamurran ilimi kamar yadda ya dace, su kuma wadanda ake koyawa suna fahimtar abinda ake koya masu. Hakanan ma ayyukan da za su iya yi jami’an ilimi suna da yawa sun kuma sha bamban.Suna ma iya yin aiki a bangarorin kamar su yadda za a tsara ci gaban koyarwa, horar da Malami,yadda za a rika bibiyar tsarin ilimi, da kuma binciken ilimi.Jami’an ilimi suna iya kasancewa wadanda suka kware a fannoni ko bangarori daban daban kamar karatun/ilimin rayuwar farko ta yaro, bangaren yaki da jahilci, ilimi na musamman, da kuma ilimin koyon sana’oi.