Hukumar tafiyar da harkokin jami’ar gwamnatin tarayya ta Oye Jihar Ekiti (FUOYE)ta kafa kwamitin mutum tara wanda zai bincike kan zargin da ake yi na mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Abayomi Fasina, da aikata badana da wata babbar jami’ar sashen ayyuka na jami’ar.
Sanarwar ta rajistaran jami’ar wadda har ila yau shi ne sakataren gudanarwar ta, Mufutau Ibrahim,ta bayyana an dauki matakin ne bayan da hukumar jami’ar ta kira taron gaggawa ranar 24 ga watan Janairu 2025.
- Annobar Cutar Murar Tsuntsaye Ta Yadu A Jihohin Filato Da Katsina
- Sin Ta Mayar Da Martani Ga Shirin Japan Na Aiwatar Da Matakan Hana Fitar Da Kayayyaki Zuwa Sin
Ta ce ta yi la’akari da labarum da kafafen sadarwa na, lamarin bincike domin aikin jarida (FIJ)da Sahara Reporters suka wallafa inda suke zargin mataimakin shugaban jami’ar ya nemi ya aikata laifin badana da Injiniya.Mrs Folashade Adebayo, mataimakiyar darkta ta sashen ayyuka na jami’ar.
Ta kara bayanin cewa “Hukumar jamai’ar ta tattauna lamarin sosai inda ta yi bayanin cewar jami’ar gwamnatin tarayya Oye- Ekiti ta shiga cikin labarai sosai saboda dalilan da basu gaskata ba, da suke neman ci gaban da jami’ar ta yi.
“Wannan ya sa hukumar zartarwar jami’ar ta kafa kwamitin bincike domin ya duba shi zarge- zargen da ake yi sosai da sosai domin su gano gaskiyar lamarin, cikin makonni uku.”
Kwamitin zai bincike kamar yadda aka bada sharuddan da za ta ayi amfani da su lokacin bincike, domin ta gano ta yaya lamarin maganganun da ake yadawa,da ake zargin abubuwan da suke da alaka da badana wanda mataimakin shugaban jami’ar ne aka ce akwai kokarin da ya yi domin ya sayi mukaman Bursar da rajistara, kana agano dalilin da yasa aka dauki maganar wadda yanzu ta zama abar maganar ta kafofin sadarwa na zamani.
Hakanan ma kwamitin an ba shi alhakin da ya yi bincike kan maganar da ake ta yadawa cewa shi Injiniya.Adebayo, musamman ma zargin da ake yi na shi mataimakin shugaban jami’ar a sake duba dukkan kokarin da aka yi da matakin da aka dauka wanda ‘yansanda, da shi kuma shugaban jami’ar na bya da sauran kan maganganun da Adebayo yay ikan mataimakin shugaban jami’ar.
Bugu da kari ta bada ayi bincike kan duk wani zargin da aka yi da duk abinda yake da alaka shi binciken.
“Hukumar jami’ar tana sa ran za ta yi amfani da rahoton binciken na kwamitin da ta kafa domin yin hakan