Gwamnan Jihar Kogi Ahmed Usman Ododo ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bada fifiko/matukar kulawa kan ilimin yara marayu da wadanda basu da galihu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yak e kaddamar da bikin bude tsarin Gwamna Ododo na kulawa da ‘yan makaranata marayu Orphan lamarin da wani tsari ne da kungiyar mataimaka na musamman na Kananan Hukumomin Jihar Kogi, ya jaddada babu wani yaron da za a watsi da shi ko a manta shi, sanadiyar mutuwar masu kulawa da shi daga Iyaye ko kuma Dangi saboda rashin kudi.
- An Kama Miyagun Kwayoyi Kan Hanyar Zuwa Birtaniya A Filin Jiragen Saman Legas
- Gwamna Radda Ya Samar Da Keke Napep Don Saukaka Zirga-zirga A Katsina
Ya ce“Akwai Allah don haka kai ba maraya bane inda ya yi kira da ‘yan makaranta wadanda suka amfana da tsarin su yadda da kan su, su kuma kiyaye duk wani abinda zai sanadin tunani da zai sa su ga, ai su basu da wata dama ko abin da za su iya yi.
Gwamna Ododo ya jinjinawa kungiyar ta mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi na musamman kan kudurin da suka dauka na taimakon wadanda basu da masu taimaka masu. Ya ce shi tsari wata manuniya ce ga tsarin nasarar gwamnatin sa wadda za ta kai ci gaba ga mutanen Karkara.
“Abinda muke yi yau anan shi ne mu nuna bamu taba yin wani kuskure kan matakan da muka dauka ba, saboda wannan Gwamnatin ta mutane ce kamar yadda ya ce.
Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki.
Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi kan kudurin sa na ci gaba da kammala duk bada wadansu mukamai na magoya bayan sa fda suke a Karkara.
Ya yi kira da mambobin kungiyar da wadanda suka amfana da taimakon kungiyar,su ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka sa a gaban su, saboda ayyukan alkahairin da suka fara zai samar da babbar gudunmawar ci gaba a wasu shekaru ma su zuwa.
“Abinda muke yi yanzu da kuma yau wadansu mutane ba za su iya gane muhimmancin sa,sai dai kuma sannu a hankali a gaba za a iya gane ashe lamarin na alkhairi ne kamar yadda ya yi bayanin gaskiyar halin da ake ciki,”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp