Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani.
Kafar yada labaran kasar ta rawaito Mista Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matukar muhimmanci a tsarin da kasar ke yi na karfafa shirin makaman nukiliya, da kuma fito na fito da duk kasashen da suka nemi tsoma baki a harkar kasarsa.
Kalaman Kim na zuwa ne bayan gwajin makaman da Pyongyang ta yi a ranar Asabar da ta wuce, domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, shi ne gwaji na farko tun bayan shugaban Amurka Donald Trumo ya sha rantsuwar kama aiki.
A bangare guda kuma Mista Trump ya ce zai sabunta huldar da ke tsakaninsa da shugaban na Koriya ta Arewa.