Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta nuna adawa da rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasar Sin, kuma za ta dauki matakan da suka dace don kare halaltattun hakkokinta da moriyarta.
Kakakin ya jaddada cewa, “Kasar Sin tana tsaye kan matsayinta ba ja da baya. Babu wanda zai yi nasara a yakin cinikayya da haraji.”
Yana mai cewa, karin harajin bangare daya na Amurka ya sabawa ka’idojin WTO. Kuma wannan matakin ba zai iya magance matsalolin Amurka na gida ba kuma mafi mahimmanci, ba zai amfanar da kowane bangare ba, balle ma duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp