Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari a unguwar Kumana da ke masarautar Kwassam a garin Galadimawa da kuma yankin Rumaya na karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna a wani sabon hari da suka kai inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu biyar.
Wasu mutane uku kuma sun samu raunuka daban-daban a yayin da ‘yan bindigar suka kai munanan hare-hare a kan al’ummar yankin.
- Gwamnan Kaduna Ɗan Amshin Shata Ne Ga Tinubu Saboda Tallafin ₦150bn — El-Rufai
- Ƙarar Kwana: Yadda Hakimin Kaduna, Sarkin Yaƙin Zazzau Ya Faɗi Ya Rasu
‘Yan bindigar da suka afka cikin al’ummomin, sun yi ta harbe-harbe a lokacin harin da suka kai a ranar Litinin, lamarin da ya jefa mazauna kauyen cikin firgici
Da yake tabbatar da harin, wani mazaunin T/wada Garmadi, Rumaya Kwassam, Mista Joel Ahada, ya yi Allah wadai da wannan danyen aikin, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin mutunta hakkin dan Adam da kare lafiyar mazauna karkara.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.