Wani ɗalibin aji biyu (200-level) a Jami’ar Ilorin (UNILORIN), da ke Jihar Kwara, ya kashe kansa a ɗakin kwanansu da ke yankin Oke-Odo, na unguwar Tanke, a Ilorin, babban birnin jihar, saboda kasa jurewa matsin rayuwa da yake fuskanta.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗalibin ya sha guba a ƙarshen makon da ya gabata bayan abokin zamansa ya tafi karatu, inda ya bar wata takarda da ke bayyana cewa ba zai iya jure wahalar da yake ciki ta tsanani ba.
- Masana Kimiyyar Sin Sun Kirkiro Sabuwar Fasahar AI Mai Hasashen Zuwan Mahaukaciyar Guguwa
- Kuɗin Fansa ₦13m, Kasonsa ₦200,000: Ɗan Shekara 50 Ya Jagoranci Garkuwa Da Ɗansa Da Iyalansa
Marigayin, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, yana karatu a Tsangayar Sadarwa ta jami’ar, kuma yana da maki 4.5 a tsarin ƙididdigar ilimi wato (CGPA) a sashen koyar da aikin Jarida kafin mutuwarsa.
An kuma samu labarin cewa ɗalibin ya rasa mahaifinsa a wasu shekarun baya, lamarin da ya mahaifiyarsa wadda tsohuwar malamar makaranta ce ta ci gaba da ɗaukar nauyin karatunsa tun daga lokacin.
Rahotanni sun nuna cewa matsalarsa ta ƙara tsananta tun bayan dawowarsa makaranta a bara, inda abokan karatunsa suka tara kuɗi domin biya masa kuɗin makaranta da kuma siya masa kayan abinci.
Duk da cewa jami’ar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, amma wani babban jami’i a makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, yana mai bayyana hakan a matsayin abin mamaki da ya jefa jami’ar cikin jimami.