Har yanzu dai ana ci gaba da ikirarin nan na tinkahon “Amurka ta zama farko”, inda a wannan karon, Amurkar ta zabi ficewa daga kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, tare da daukar batun kare hakkin bil’adama na kasa da kasa gaba daya a matsayin wani makami na nuna “babakeren Amurka.”
A cikin wani binciken ra’ayoyin jama’a na kafar watsa labarai ta CGTN, kashi 86.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi sun yi imanin cewa, Amurka tana fama da mummunar matsalar amfani da bindiga; kashi 73 cikin dari na masu bayyana ra’ayin kuma suna tunanin cewa, Amurka ta shiga mummunar matsalar shan muggan kwayoyi yayin da kashi 72.3 cikin dari na mutanen kuma suke ganin wariyar launin fata a matsayin wata babbar matsala da ke addabar Amurka.
Binciken ya gano cewa, kashi 72.5 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyin a sassan duniya sun dauki Amurka a matsayin kasa mai mamaye komai da komai, yayin da kashi 64.9 daga cikinsu kuma suka soki Amurka saboda yawan amfani da kare ‘yancin bil’adama a matsayin wata hujjar murkushe wasu kasashe.
Kazalika, kashi 85.2 cikin dari na masu bayyana ra’yoyin sun yi imanin cewa, wannan matakin da Amurka ta dauka ya illata tsarin kasa da kasa da ya shafi Majalisar Dinkin Duniya, kana kashi 81.6 cikin dari na mutanen sun soki Amurka saboda sadaukar da muradun kasa da kasa don cimma matsakaitan muradunta na kashin kai, wanda zai yi matukar lalata tsarin daidaito da tabbatar da adalci a tsarin tafiyar da mulkin duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)