A shekarar 2025 da muka ciki, ita ce karo na farko da aka yi murnar Bikin Bazara na sabuwar shekarar al’ummar Sinawa bayan da aka shigar da shi cikin jerin bukukuwan al’adun gargajiya da bil’adama ya gada a duniya. Don haka ana iya cewa, kasuwa ta samu tagomashi a kasar Sin.
Yawan bulaguron yawon bude ido da aka yi a cikin gida ya kai miliyan 501 a kasar Sin, masu yawon bude idon sun kashe sama da kudin Sin RMB yuan biliyan 677, adadin da ya karu da kashi 5.9% da kuma kashi 7.0% kan na shekarar 2024. Yawan shige da fice da mutane suka yi a kasar Sin ya kai miliyan 14.366, wanda ya karu da kashi 6.3% kan na bara.
- Mbappe Da Bellingham Ba Za Su Buga Wasan Da Real Madrid Za Ta Kara Da Leganes Ba
- Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara
Haka zalika, yawan makudan kudaden sayen tikitin kallon fina-finai da yawan kallon fina-finai a lokacin hutu na murnar Bikin Bazarar bana sun kafa tarihi, yayin da yawan kudaden sayen tikitin kallon fina-finai a kasar Sin ya fi na Arewacin Amurka, inda a halin yanzu ya zama na daya a duniya.
Kamar yadda masharhantan kasa da kasa suka fada, tattalin arzikin kasar Sin ya samu sabon kuzari a Bikin Bazara na gargajiya, lamarin da ya nuna cewa, an samu karin kuzari da juriya a kasuwar kasar Sin.
Yadda harkokin sayayya na kasar Sin suka fara da kafar dama, ya sanya an kara sanin ci gaban da tattalin arzikin kasar Sin ke samu. Kwanan baya, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya kyautata hasashensa kan bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ta shekarar 2025 da ta 2026. Haka kuma, kamfanonin Faransa da Jamus sun kara habaka cinikinsu a kasar Sin. Kamfanoni masu jarin waje da dama sun bayyana hasashensu kan harkokin zuba jari a duniya a shekarar 2025, inda suka ci gaba da yin na’am da kasuwar kasar Sin.
Sakamakon yadda kasar Sin take ci gaba da zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, da kyautata bude kofa ga ketare bisa matakin koli, ya sa kasar ta Sin za ta ci gaba da kara azama kan bunkasar tattalin arziki. Za kuma ta ci gaba da nuna kuzari kan raya kanta tare da amfanar da duniya baki daya. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp