Za’a gudanar da bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya karo na 9, da daren gobe 7 ga wata, bisa agogon kasar Sin, a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin, tare da sanar da bude gasar.
Kana da tsakar ranar gobe, shugaba Xi zai kuma shirya shagalin maraba da zuwan shugabannin kasashen waje don halartar bikin bude gasar a kasar Sin.
- Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata
- Zulum Ya Jagoranci Dawowar Ƴan Gudun Hijira 7,790 Daga Chadi
Daga cikin shugabannin kasashen waje da suka zo kasar Sin don halartar bikin, akwai Sultan na kasar Brunei Haji Hassanal Bolkiah Mu’izzaddin Waddaulah, da shugaban kasar Kyrgyzstan Sadyr Japarov, da shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari, da firaministar kasar Thailand Paetongtarn Shinawatra, da shugaban majalisar dokokin kasar Koriya ta Kudu Woo Won-shik.
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ko CMG a takaice, zai gabatar da yadda za’a gudanar da bikin kai-tsaye, yayin da kafar yada labarai ta Xinhuanet ma za ta ruwaito rahotanni kai-tsaye game da bikin.
A yau Alhamis, shugaba Xi Jinping ya gana da firaministar kasar Thailand Paetongtarn Shinawatra da Sultan na kasar Brunei Haji Hassanal Bolkiah Mu’izzaddin Waddaulah a birnin Beijing na kasar Sin. (Murtala Zhang)