Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi kira ga mahukuntan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (KAEDCO) da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) da su kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu wacce ta haifar da matsananciyar rashin wutar lantarki a jihohin Kaduna, Sakkwato, Kebbi, da Zamfara.
Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Balarabe ce ta yi wannan kiran a lokacin da ta jagoranci wani muhimmin zama a ranar Alhamis tsakanin shugabannin kamfanonin wutar lantarki na Kaduna da shugabannin kungiyoyin kwadago a gidan gwamnati da ke Kaduna.
- Babban Jami’in JKS Ya Yi Kira Da A Ci Gaba Da Kawar Da Ayyuka Mara Ma’ana
- Ko Barcelona Za Ta Iya Sake Zazzagawa Valencia Ƙwallaye 7 Yau?
Wannan zama da gwamnatin jihar Kaduna ta jagoranta, wani yunkuri ne na kawo karshen yajin aikin da ma’aikatan wutar lantarkin ke yi kan sallamarsu da kamfanin ya yi a ranar Lahadin da ta gabata.
A yayin zaman, Dakta Balarabe ta jaddada tsananin tasirin da katsewar wutar lantarkin ke yi ga muhimman ayyuka, musamman harkokin kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a fadin jihohin da abin ya shafa.
Ta bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su maido da wutar lantarki yayin da ake ci gaba da tattaunawa don samun maslaha.