Babban Bankin Nijeriya CBN, ya mayarwa da masu hada-hadar musayar kudi BDC da suka biya kudadensu na sake sabunta lasisin su a 2025 bayan damar daga masu kafa da Bankin ya yi.
Hakan na kunshe ne, a cikin wata Takarda da Mukaddshin Riko na sashen kudi da tsare da sanya ido na Bankin John Onojah ya sanya hannu.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi
- Gidaje Da Dabbobi Sun Ƙone A Yayin Da Gobara Ta Tashi A Wani Ƙauyen Kano
Takardar ta sanar da cewa, da masu hada-hadar musayar kudin da suka da suka biya kudadensu su rubutawa Bankin bukatar mai do masu da kudadensu.
A cewar Bankin na CBN, damar ta daga kafar da wadda ta kara aiki nan take, na daya daga cikin sauyawa zuwa sabuwar dokar hada-hadar musayar kudade ta Bankin.
“Ana son a sanar da masu hada-hadar musayar kudaden cewa, bisa ka’idar sanya ido ta dokar aikin hada-hadar musayar kudade ta kasa ta 2024, da kuma kan ci gaba da sauyawa zuwa sabuwar dokar hada-hadar musayar kudade ta Bankin na CBN, CBN ya amince da damar daga masu kafa sabunta bayar da lasisin na 2025, wanda zai fara aiki, nan take.” Inji Takardar.
“Kowannen masu hada-hadar musayar kudade da aka san da zamansu da suka biya kudinsu na sake sabunta lasisinsu na 2025, an shawarce su da su rubuta zuwa ga Daraktan sashen kudi da tsare da sanya ido na Bankin, domin su karbi kudansu, da aka dakatar da biyan kudi, zuwa cikin asusunsu.” Inji Takardar
Takardar ta bayar da tabbacin cewa, Bankin na CBN, har yanzu a tsaye yake akan kafarsawajen ganin ya samar da daidaito da bin ka’ida, musamman wajen gann ana gudanar da hada-hadar musayar kudade na waje a kasuwar musayar kudi.