Bisa sabon rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar ya nuna cewa, farashin kayan abinci ya yi tashin guaron zabi a daukacin fadin kasar.
A yanzu haka, a cewar rahoton farashin na kayan abinci ya karu daga Naira 2,862.14 a cikin watan Nuwambar 2024 zuwa Naira 2,920.13 a watan Dismabar 2024.
- Ba Mu Amince Da Yi Wa Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Shari’a A Sirrance Ba
- Gidaje Da Dabbobi Sun Ƙone A Yayin Da Gobara Ta Tashi A Wani Ƙauyen Kano
Hauhawan farashin na kayan abincin daga shekara zuwa shekara, ya kai kashi 91.6 a cikin dari a watan Disambar 2023 wanda ya kai Naira 1,524.63.
A cikin bayanan ha Hukumar ta NBS mai taken, ‘ Wasu kayan abinci da aka zabo don yi duba a kansu a watan Disambar 2024’, na fitar da shi ne, a ranar 24 na watan Janairun 2025.
Wannan hauhawan na farashin kayan abincin, ya jefa rayuwar miliyoyin iyalai da kuma daliban kasar, a cikin wani mawuyancin rayuwa.
Kazalka, matsalar ta sanya wasu iyalai da dalibai da dama a kasar yin kokarin jurewa matsin rayuwar da suke ci gaba da fuskanta, wanda hakan yak e kuma kara zamowa, babbar barazana ga rayuwarsu.
Bisa fashin baki da rahoton ya yi ya nuna cewa, a shiyoyi shida na kasar, banbancin hauhawan farashin na kayan abincin, ya sha ban ban, inda a yakin Kudu Maso Yamma, lamarin na hauhawan farashin kayan abincin, ya fi yin kamari.