Kasar Sin ta yi watsi tare da nuna kin amincewarta da tsegumin da aka yi mata daga bangaren Amurka, inda sakataren harkokin wajen Amurkar, Marco Rubio ya yi wasu zarge-zarge marasa tushe balle makama a kan kasar ta Sin, yayin da yake ziyara a yankin Latin Amurka da Caribbean.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan a yau Juma’a, inda ya kara da cewa, kalaman marasa tushe daga bangaren Amurka, wadanda suka karkata zuwa tunanin yakin cacar-baka da nuna son zuciya, zarge-zarge ne kawai na yamadidi a kan kasar Sin da aka kitsa da nufin haifar da sabani tsakaninta da kasashen da abin ya shafa na Latin Amurka da Caribbean, wanda kuma hakan tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, da kuma gurgunta hakkoki da moriyar kasar Sin ta halaliya da kuma muradunta.
Game da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da yankin na LAC kuwa, mai magana da yawun ma’aikatar ya ce, kasar Sin ta kuduri aniyar karfafa abokantaka da hadin gwiwa tare da kasashen na LAC bisa tsarin mutunta juna, da daidaito, da cin moriyar juna, da bude kofa, da hada kai, da sauran harkokin hadin gwiwar samun nasara ga ko wane bangare. (Abdulrazaq Yahuza Jere)