Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.”
Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka yi wajen habaka aikin wurin ajiye kaya da jiragen kasa yana nufin karin inganci da rage tsadar gudanar da ayyuka, kuma yana taimakawa wajen biyan bukatun al’ummar kasar wajen yin zirga-zirga.”
Tun lokacin da aka kaddamar da shi a shekarar 2018, layin dogon wanda kasar Sin ta gina ya ci gaba da bunkasa kasuwar dakon kayayyaki da kuma fadada ayyukansa na hidima, ciki har da ayyuka masu inganci kamar sufurin kayayyakin sanyi, da jiragen kasa masu jigilar mazauna kauyuka, da jiragen kasa na musamman don jigilar motoci. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp