ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
Tinubu

A cikin wannan makon ne Editanmu Bello hamza ya tattauna da wani matashi dan rajin tabbatar da dimikradiyya a Afrika, mai suna Kwamared Bishir Dauda. Ya yi bayani da dama musamman a kna korafin da was uke na cewa, Shugaba Tinubu ya yi watsi da Arewa wajen gudanar da ayyuklan raya kasa, ga dai yadda hirar ta kasance.

Za mu so ka gabatar mana da kanka

  • Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare
  • Gwamnati Na Ƙoƙarin Tsoratar Da Ni Don In Shiga APC – Sanata Tambuwal

Sunana Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina,dan rajin kare Dimokaradiyya,’yancin dan Adam, kishin Nijeriya da Afirika . Nine babban daraktan kungiyar farar hula mai yaki da cin hanci da rashawa mai suna ‘Citizens Participation Against Corruption Initiatibe’. Kuma ina cikin kungiyoyin farar hula da dama a gida Nijeriya da kasashen Afirika.

ADVERTISEMENT

 

Me zaka ce a kan masu korafe-korafe a kan ayyukan Shugaba Tinubu a Arewa?

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

Akwai wasu tsaffin ‘yan siyasa daga yankin Arewacin Najeriya,wadanda ke ci da gumin ‘yan Arewa. Wadannan tsaffin ‘yan siyasa, yanzu alkadarinsu ya riga ya karye, ba su da wani abu da ya rage illa su rungumi siyasar kabilanci da bangaranci.

Ba tsaffin ‘yan siyasa kawai ba ne. Gungu-gungu ne. Wasun su, tsaffin ‘yan boko ne. Wasu ‘yan Kasuwa. Wasu ma ba wata sana’a ko wani aiki da suka taba yi a rayuwarsu da ya wuce ci da gumin Arewa . Wani abu da ya hade su shi ne, mafi yawansu sun samu damar da za su taimaki Arewa ko mutanen Arewa, amma suka ki. Misali, a cikin irin wadannan mutane, babu maras sa kunya,irin wadanda suka rike mukamai a gwamnatin marigayi Shugaba Buhari. Ire-iren wadannan mutanen har suna da bakin magana? Yanzu har wani wanda ya taba rike mukamin minista a gwamnatin Buhari na da bakin magana cewa an ki kammala hanyar Abuja zuwa Kano? Me yana su gama ta lokacin da sunan mulki? Me ya hana su gama aikin hanyar Kano zuwa Katsina ko Kano zuwa Kongolam? Me ya hana su gama hanyoyi da yawa a Arewa?

Abin takaici shugabannin wadannan kungiyoyi na dattawan Arewa, babu damar da ba su samu ba. Amma Fisabilillahi in da sun yi amfani da damar da suka samu, da yanzu za ai magana akwai marabarata a Arewa ko matasa masu bangar siyasa? Wasu gwamnoni cikin su. Yanzu misali, in banda me tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekaru zai yi a kungiya? Wanda yai gwamna shekara 8, yai minista, yai sanata, kuma maida kan shi baya ya dawo kungiya? Kuma kungiya ba irin ta su tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter ba. Ai a duniya, wadanda suka taba rike mukaman siyasa na kafa gidauniya amma ba kungiyar siyasa ba. Ba kungiyar neman abinci ba da tattaunawa kan mukaman siyasa. Gidauniya aka sani mai yaki da cututuuka,ko mai bunkasa ilmin mata da yara da sauran matsaloli ba kungiyar assasa kabilanci ba da siyasar ci da ceto

Wadannan mutanen ta kare masu ne kawai. Ba su da abin fada shi ne suka dawo suka dauki kahon tsana suka kafa ma gwamnatin Shugaba Tinubu. Babu wani kishin Arewa a tare da su.

 

Wadanne Ayyuka Tinubu Ya Gudanar A Arewa?

Tunda aka kirkiri Nijeriya,ba ai shugaban da ya dauko hanyar ‘yantar da Arewacin Nijeriya ba, kamar shugaba Tinubu. Misali, su wa za su fi cin gajiyar hukumar kiwo? Arewa an santa da noma da kiwo. Tinubu ya kirkiri hukumar kiwo ya dauko minista daga Arewa Mukhtar Idi Maiha ya damka amanar wurin. Ya dauko mutane masu daraja kamar Farfesa Attahiru Jega ya sanya a wurin domin a zamanantar da kiwo, a kawo karshen fadace fadace tsakanin manoma da makiyaya, sannan Nijeriya ta samu karuwar kudaden kasashen waje. A gabanka, lokacin babbar Sallah, shugaban mulkin sojar janhoriyar Nijar ya hana a shigo da dabbobi a Nijeriya. Wannan babban sako ne cewa mu tashi mu farka. Kuma Arewacin Nijeriya za mu dogaro da kanmu harma mu ciyar da Nijeriya da nama da madara idan muka ci gaba da ba gwamnatin Tinubu goyan baya.

Shugaba Tinubu ya bude iyakokin da Buhari ya kulle, abinci ya karu a kasa. Shugaba Tinubu ya ba da ayyukan hanyoyin da gwamnatin Buhari ta watsar kamar layin dogo daga Kano zuwa Maradi, hanyar Sokoto zuwa Badagary, Akwanga zuwa Gombe, Kafur Marabar Kankara zuwa Gidan Mutum Daya, Kano zuwa Kongolom da sauran su. Ana ci gaba da aikin bututun iskar gas daga Ajakuta zuwa Kano, ana ci gaba da aikin hako mai a Kolmani. Shugaba Tinubu ya ba Arewa mukaman da sune gwamnati. Ministan tsaro guda biyu duk Arewa ne. Mai ba shugaban kasa akan tsaro dan Arewa ne. Kuma ba wanda aka hana yai aikin shi. Misali, ko Hasidin Iza Hassada ba zai ce kashe ‘yan ta’adda dubu goma sha uku ba komi bane. Ko ‘yanto mutanen da akai garkuwa da su sama dubu sha daya ba daidai ba ne.

An ba mu mukamin ministan kiwon lafiya da walwala, Muhammad Ali Pante da duniya ke alfahari da shi saboda an tabbatar da kwarewarsa. Misali, cikin shekaru 2 kawai, an gyara kananan asibitocin guda 500 a jihohin Arewa. An sakar fannin kiwon lafiya matakin farko kudi Naira Biliyan 20 a Arewa domin rage mutuwar mata masu haihuwa da yara kanana. An yi ma mata dubu 4 fidar haihuwa (CS) kyauta. An yi miliyoyin yara allurar rigafin kyanda,zazzabin cizon sauro da farar masassara. Mutane miliyan daya da dubu dari tara masu dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki na ci gaba da samun magani duk da datse tallafi da gwamnatin Amurka ta yi. da sauran su.

Tinubu ya ba mu karamar ministan Ilmi, Suwaiba. A shekarar 2024, gwamnatin shugaba Tinubu ta ba kowace jihar Naira Miliyan 598 ta horas da malamai, ta gina makarantu na zamanin na firamare 37 da sauran su. Hukumar TETFUND baki daya hannun ‘yan Arewa take. Babban Sakataren hukumar Sonny Echono da shugaban Board din Aminu Bello Masari duk ‘yan Arewa ne,kuma dubi irin aikin da ake a wurin?

Batun ba dalibai lamani,abi ne mai kyau da zai amfani ‘ya’yan talakawa su sami ilmi mai inganci domin fita daga kangin talauci. Tsaffin Arewa masu ci da gumin Arewa ba su damu da ilmin ‘yan uwansu ba. Sun fi kyautata ma kawalai, karuwai da ‘yan bangar siyasa.

Idan ka koma bangaren aikon gona, Abubakar Kyari da ayyukan da ake. Takin kawai a shekarar 2024 karkashin tsarin AgriPocket sun ba manoma miliyan 2 a kan rangwamen farashin kashi hamsin. Babban Bankin Nijeriya, ya rama manoma da ba na boge ba buhun taki miliyan biyu da dubu dari biyu.

Saboda haka farfaganda ce ta siyasa masu fadar ba a yi da Arewa. Kamata yai su fito fili su ce ba a yi da su kawai.

 

Kiranka ga al’ummar Arewa?

To ni kirana ga matasan Arewa, shi ne, kada su bari masu ci da ceto su maida su makaman siyasa. Tinubu ya ce kowa zai iya zama mai ilmi. Ko farfesa kake so, ga kofa an bude. Saboda zabi ya gare ka ka bi hanyoyin da aka tanada domin amfana da tsare-tsaren gwamnati, kamar NELFUND da sauran su.

Mutanen Arewa mu sani zaman lafiya da hadin kan Nijeriya ya fi burin wani dan siyasa. Maganar kabilanci da bangaranci mu barta, saboda kasashe da yawa sun tarwatse,an yi yake yake a kasashen Afirika da dama saboda wasu ‘yan siyasa sun fito da batun kabilanci.

Rwanda, Saliyo, Liberia, Ibory Coast da sauran su duk sun danin sakamakon siyasar banza ta kabilanci. Mulki zai dawo a 2031 ba 2027 ba, kuma shugaba Tinubu ne yakamata a sake zabe saboda shi ya gano matsalar Najeriya,kuma ya dauki hanyar magance ta.

Tinubu
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
Rahotonni

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Rahotonni

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Next Post
Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Darakta-Janar Na NTA Da Wasu Daraktoci

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Darakta-Janar Na NTA Da Wasu Daraktoci

LABARAI MASU NASABA

NSCDC Ta Kama Ɓarayin Mota, Ta Ƙwato AK-47 A Abuja

NSCDC Ta Kama Ɓarayin Mota, Ta Ƙwato AK-47 A Abuja

September 15, 2026
Gwamnatin Zamfara Za Ta Mayar Da Yara 453,602 Makaranta

Gwamnatin Zamfara Za Ta Mayar Da Yara 453,602 Makaranta

September 15, 2026
’Yan Ta’adda Sun Kai Wa Ƙauyuka 2 Hari A Adamawa

Boko Haram Sun Kashe Mutane 4 Tare Da Ƙone Gidaje A Adamawa

September 15, 2026
Wani Mutum Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kogi

’Yan Ta’adda Na Shirin Kai Hare-Hare Makarantu, Wuraren Ibada Da Sansanonin NYSC – ’Yansanda

September 15, 2026
Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Masallacin Sheikh Lukuwa Bayan Harin Da Aka Kai Masa

Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Masallacin Sheikh Lukuwa Bayan Harin Da Aka Kai Masa

September 15, 2026
Hannun Jari: Dangote Ya Yi Wa ’Yan Nijeriya Alƙawarin Samun Gaggwaɓar Riba

Hannun Jari: Dangote Ya Yi Wa ’Yan Nijeriya Alƙawarin Samun Gaggwaɓar Riba

September 15, 2026
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Arziƙin Dangote Ya Haura Dala Biliyan 50 Bayan Fara Sayar Da Hannun Jarin Matatarsa – Forbes

September 15, 2026
Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

September 14, 2026
Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

September 14, 2026
Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

September 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.