Albarkacin bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 dake gudana a birnin Harbin na Sin, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa, Thomas Bach ya ziyarci cibiyar yada labarai ta gasar a jiya Juma’a, kuma ya yi hadin kai da shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin mallakin kasar Sin, wato CMG, Shen Haixiong, don bai wa runkunin na CMG damar tsarawa da kuma sarrafa watsa labarun gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Milan da Cortina d’Ampezzo ta shekarar 2026.
Shen Haixiong ya ce, gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya da ake shiryawa a birnin Harbin, wata kasaitaciyyar gasa ce ta kasa da kasa da Sin ta shirya bayan gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. A tsakar wannan rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a yayin liyafar maraba da muhimman baki wadanda suka halarci bikin bude gasar cewa, Harbin zai gabatar wa duk fadin duniya wata gasar wasan motsa jiki mai kayatarwa da ke kunshe da salo irin na Asiya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp