A yau Asabar, 8 ga wannan wata da safe, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aiki na kwamitin JKS da gwamnatin lardin Jilin a birnin Changchun dake lardin Jilin. Bayan kammala sauraro, shugaba Xi ya yi jawabi inda ya jaddada cewa, ya kamata hukumomin lardin Jilin su aiwatar da shirin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin a dukkan fannoni a sabon zamani da kwamitin tsakiya na JKS ya tsara, da tabbatar da tsaron kasar a fannoni 5, da maida hankali ga aikin samun ci gaba mai inganci, da bin tsarin tunanin sabon ci gaba, da bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima a dukkan fannoni, da amfani da dama, tare da kara kokarin kirkire-kirkire don ba da gudummawa ga samun nasarar zamanantarwa irin ta kasar Sin.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, samun ci gaba mai inganci yana da nasaba da yin kirkire-kirkire da tabbatar da bunkasar sauran sha’anoni. Don haka, ya kamata a ci gaba da raya tattalin arziki da kyautata tsarin raya sana’o’in gargajiya da na zamani, inda ta hakan za a kafa tsarin sana’o’in zamani mai salon musamman na lardin Jilin. (Zainab Zhang)