Albarkacin ranar masoya ta duniya da Hukumar kula da al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta fitar da 14, ga watan Febarairun kowacce shekara a matsayin ranar masoya ta duniya.
Jaridar LEADERSHIP ta sanya gasar gajerun labaran soyayya na Hausa tare da bayar da kyautar kuɗi har ₦50.000 da ₦25.000 da kuma ₦10.000 ga waɗanda suka yi nasarar lashe gasar a mataki na ɗaya da na biyu da na uku, tare da wallafa labaran da suka yi fice a Jaridarmu ta mako da shafukanmu na yanar gizo.
- Fadawa Soyayya Saboda Tausayin Budurwa Da Yadda Abin Ke Sauyawa
- Trump Zai Fuskanci Tirjiya A Duniya, Ba Soyayya Ba – Shehu Sani
Sharuɗa da ƙa’idojin shiga gasa:
1. Rubuto labarin soyayya mai taba zuciya ko ban-tausayi da ya faru da kai wanda bai gaza kalmomi 500 ba.
2. Ka kasance cikin Mabiya a duka shafukanmu na sada zumunta.
3. Wallafa labarin a kasan wannan sanarwar a ɓangaren tsokaci.
4. Wallafa labarin a shafinka na sada zumunta na facebook tare da makala #tak na #GasarLabarunSoyayya #LeadershipHausa #GasarLeadership
5. A kiyaye ƙa’idojin Rubutun Hausa da kuma amfani da daidaitacciyar Hausa da aka amince a yi amfani da ita a hukumance.
6. Ka tabbatar ka sanya lambar wayarka da sanya adireshinka na Imel a kasan labarin da ka kawo, ka kuma turo mana ta Imel dinmu na: [email protected]
Za a rufe karɓar gajerun labaran a ranar Alhamis mai zuwa 13/02/2025 da karfe 12, na rana.