Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, cikin sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da matsalolin da wasu mazan ke fuskanta game da wasu matan a yanzu, musamman ta fanni soyayya, duba da yadda ‘yan mata ke kai tayin soyayya ga samari sabanin lokutan baya.
- KANSIEC Ta Sauya Lokacin Zaben Kananan Hukumomin Kano Zuwa Oktoba
- Rikicin Masarautar Kano: Sarki Bayero Ya Ƙaddamar Da Sabunta Ginin Fadar Nassarawa
Akwai ‘yan mata da dama wadanda suke zuwa wajen saurayi su bayyana soyayyarsu wanda wani sa’in har mazan suke ganin tilastawan matan da lallai sai namiji ya karbi tayin soyayyarsu, wanda kuma ganin hakan ke sa wasu mazan jin tausayin ‘yan mata su kulla alaka da su ko da kuwa babu soyayya, har saurayi ya ci gaba da bawa mace kulawa tare da yawaita kashe mata wasu kudade duk dan ya kyautata mata, ba wai dan yana son ta ba, wanda ita kanta ta san da hakan.
Sai dai kuma wasu daga cikin samari masu aikata hakan sun fara kokawa game da hakan, sakamakon sauyawar da su matan suke yi yayin da tafiya ta yi tafiya, kamar ta hanyar fara rokonsu wasu kudade masu yawan gaske na anko ko na karin shekara da dai sauransu, da zarar saurayi ya ki yi, ko ya ce ba shi da kudin da mace ta tambaya sai ta ji haushi karshe ma magana ta gagara tsakaninta da shi har ta kai ga gaba.
Hakan ya sa mazan kan rasa gane gaskiyar al’amarin game da su matan musamman masu aikata hakan, shin hakan soyayya ce ko kuwa yaudara ce?. Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; Ko me za a kira hakan da shi?, Shin laifin waye tsakanin saurayin da kuma budurwar?
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka: Sunana Rukayya Abubakar Shawai:
Gaskiya ba so bane, tsantsar yaudara ne wata kila akwai abin da ta hango ko akwai wani buri da ta ke son cimmawa, kuma ba ta da wata hanya wacce ta wuce ta bullo masa ta bayen fage ta hanyar yaudararsa da sunan soyayya. Laifin shi ne; Da farko dai a fuska ta addini ba laifi bane idan mace ta ga namiji tana son shi ta furta masa, a addinance aka ce za ka iya san mutum domin kudi ne, ko kyau ne, amma mafi a’ala ka so mutum domin Allah, kin ga kenan addini ya warware mana komai, amma a wannan gabar sai aka ce ka so mutum domin Allah, saboda watakila arzikin nasa na lokaci ne, ko kuma kyawun nasa ya dishe, idan hakan ta faru kin ga kenan za ta iya rabuwa da shi, ina ga abin da ya kamata yayi shi ne ya rabu da ita kawai. Eh! to, shawarar da zan bada ita ce su daina gaskiya, saboda samarin na yanzu su ma a cikin kaso dari to rabi duk ‘yan bana bakwai ne, wala’alla rokon da ‘yan matan ke musu suna basu to fa idan ki ka hadu da dan duniya ya bada ki, ya baki gobe, to jibi fa dole shi ne zai ro’ke ki, kuma ai ba zai ro’ke ki ki kasa bashi abin da ya nema ba, dalili kuwa shi ma kin roke shi ya baki, idan ma ba ki amince ba zai iya bin ki ta karfi, kin ga a wannan gabar zan iya cewa ke ki ka yi sanadiyyar durkushewar rayuwarki.
Sunana Zainab Ahmad Yusuf (Zinariya):
Mafi akasari hakan ba ta fiya faruwa ba idan mace ce ta fara cewa tana son shi, shi kuma gudun wulakanci ya biye mata. Laifinsa ne akwai matan da dan su kori maza suke cazarsu kudi, mu mata muna da wata irin zuciya mai tausayin wanda take so idan har mace tana yi wa namiji so na hakika ba za ta taba tambayar shi abin da ta san ya fi karfin shi ba, Idan har namiji ya ga mace tana yawan tambayar shi kudi masu nauyi to, ba son shi take ba, kawai abin hannunsa take so. Shawarata ga samari idan za su yi soyayya su dinga tsayawa iya matsayinsu da kamanta gaskiya akan komai, da yawa suna nunawa sunada hali sai kuma mace ta tambaye su, su ce ta fiya san kudi. Shawarar da zan bawa mata masu irin wannan halayyar shi ne; su ji tsoran Allah su kama mutumcin kansu, yana daga cikin abin da yake zubdawa mace kima wajen da namiji shi ne tambayarsa kudi da dora masa nauyin da yake kan iyayenki bayan ba aurenki yayi ba.
Sunana Yareema Shaheed, Jiha: Kano:
A gaskiya duk budurwar da za ta dinga rokon namiji abubuwar bukatarta na yau da kullum kamar anko da dai sauransu to, ba son shi take ba kudinsa take so domin zuwa wani lokaci za ta iya rabuwa da shi in ta gama samun abubuwan da take so. Idan namiji ya yi karo da irin wannan budurwar kar ya amshi soyayyarta ya barta kawai domin za ta iya sashi cikin tashin hankali a karshe. Kira na ga ‘yan mata da su ji tsoron Allah, su sani duk wanda ya ci amarnar dan’uwansa to Allah yana nan a madakata, don haka su daina roko da yaudara.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya hakan yana iya zama soyayya ta gaskiya kuma hakan yana iya zama soyayyar jari hujja,wanda ganin yana da abun duniya ya sa suke son shi ba wai don Allah ba ko kuma soyayyar gaskiya ba. To magana ta idan mutum ya samu kansa a wannan halin hali ko yanayi ya kamata ya nutsu sosai ya kuma yi binciken kwakwaf domin gane gaskiyar al’amarin, idan ta tabbata soyayyar gaskiya ce to babu laifi mutum ya so mai son shi. To magana ta gaskiya budurwa take shigarwa saurayi bukata sam-sam bai dace ba, domin rashin kama kaine yake jawo haka,.kuma a lokuta da dama hakan yana zama silar lalacewar tarbiyya budurwa, domin akwai samarin da ba sa tsoron Allah da za su iya yi wa budurwa duk bukatar da ta zo da ita amma suma za su mika bukatar su gare ta, daga karshe nake addu’ar Allah ya kawo mana karshen irin wannan matsala ta tabarbarewar tarbiyya da ta zama ruwan dare a cikin al’umma yanzu.
Sunana Kueen-Nasmah, Daga Jihar Zamfara:
Kai tsaye ba zan bawa hakan suna ba, domin ya danganta daga kudurin dake ran mace game da hakan a lokacin bayyana soyayya, da ma ita zuciya ko ta namiji ko mace duka idan ana kyautata maka za ka ji, a ranar da aka gaza kuwa za ka ji haushi, kin ga kenan wannan dabi’a ce da ‘yan’adam ba a ware jinsi daya a ciki ba, sai a samu wasu su fi hakurin haka. Amma idan muka duba ta wata fuska ƙwadayi ne, ta wata fuska kuma soyayya ce, mai sonka ne ma zai so abun ka, kuma zai damu idan ya rasa wani abu daga gare ka. Tabbas wannan ba laifin kowa ba ne sai na namiji shi da har ya fara kula ta bayan ya san ba sonta yake yi ba, ita mace fadawa so bai mata wahala ballantana ma a ce wanda take so yana kula ta, kuma har ya kai ga kyautata ma. A kowane hali idan ka san baka son mace kawai kar ka bata kofar da za ta rabe ka ko na minti daya, ka bar ta za ta saba da rashinka har ta koyi kula wani, wannan shi ne babban taimakon da za ka yi mata, ba wai ka nuna mata kulawa bayan ka san ba haka ba ne. Gare ku mata ma su zuwa ga maza da soyayya duk da ba a son ku, ki sani ke mace ce mai daraja, kula wanda baya sonki ba zai haifa miki da mai ido ba, domin kuwa za a wayi gari baya girmama ki domin rokar wannan soyayyar ki ka yi. Ki saba da mika soyayyarki ga wanda ke sonki ba wai wanda baya sonki ba.
Sunana Usman Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
Hakan tana faruwa sau tari (especially) ga mazajan da ba su san darajar soyayya ba, domin hakan idan tana faruwa rashin sanin darajar soyayyar ne yake kawo haka. Domin shi wanda yake sonka ai kai yake so ba wani abin hannunka ba dan haka wannan ba soyayya bace za mu iya kiranta da yaudara ce soyayyar gaske ba haka take ba. Wannan ai babban laifi ne ga wannan saurayin da hakan ta faru da shi domin sai ya kula ta ai za ta kawo mai uzurinta dan haka laifin shi ne. Ni dai shawara ta ga irin wadannan ‘yan matan shi ne ya kamata su san me ake nufi da daraja da kima a kankansu domin ba mutuncinki bane ba ma ki ga saurayi ma ki ce wai kina son shi ba, koda kin ce kina son shi ya amince dake wani kai uzurirrikanki gurinsa ai ba naki bane namiji ba shi da rowa idan ki ka yi hakuri zai yi miki, dan Allah ‘yan mata a lura a kiyaye.
Sunana Asiya Abdullahi,
Daga Jihar Kaduna:
A gaskiya hakan tana faruwa sosai, sai dai kuma na ce laifin namiji ne, domin shi ya ba ta damar hakan, idan har nmiji baya son mace bai kamata ya nuna mata kulawa ba, kamata yayi ya nisance ta ko dan ma ta daina jin abin da take ji a knsa, ba wai ya rika kusanto ta gare shi ba, yana kara sakawa tana jin sonsa a zuciya. Abu na gaba shi ne; muddin mace tana son namiji ba za ta iya karbar abun hannunsa ba da zummar roko, sai dai idan har shi ya ba ta domin kyautatawa, amma idan mace za ta rika rokon namiji anko ko wasu kudade masu yawa to, daman baya cikin jerin wanda take so ta mayar da shi ne bankinta har sai ta gama cimma burinta. Shawarata a nan ya kamata samari idan sun ci karo da macen da take son su kuma ba sa son ta, tun a farko su sanar da ita cewa babu wannan soyayyar a zuciyarsu, kuma su ba ta hakuri ta nemi wani kar su ci gaba da nuna mata soyayyar karya.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano:
Abin zai iya zama ruwa biyu wata soyayya ce ta gaske sai dai kawai zaman da suka yi da shakuwar da suka yi ya ke sa wa take ganin sun riga da sun zama daya ta inda babu wani abu da za ta iya boye masa, sannan a wannan lokacin gani take ma wani abin ko a gida idan ta ce ayi mata ba za a yi mata ba, kun dai san yadda so yake juya mutum. Daya bangaren kuma wasu matan sukan jawo soyayyar saurayin domin ganin yanada hali da kuma samun biyan bukatarsu sai daga baya idan sun gama cimma bukatarsu sai su ‘yan matan su jawo sanadin da saurayin zai ce baya son su. Shawarata a nan ita ce kai saurayi idan ka ci karo da irin wannan to kayi taka-tsan-tsan sannan ka kwana da sanin cewa komai zai iya faruwa domin ko ni da nake wannan rubutun ta faru da ni duk da ni ba mai kudin bane, sabida ai ba sai da kudi ake morar namiji ba. Shawarata ga mata masu wannan dabi’ar ita ce su ji tsoron Allah su so mutum don Allah ko dan al’adar mu ta malam bahaushe wajen gujewa wulakanci da kuma gujewa fadawa tarkon shaidanun samarin wannan zamanin, domin wasu samarin ma za su iya kashewa mace fiye da abin da ta nema ma duk domin ya bata tarbiyar ta, ina kuma ga a ce ita ce ta kawo kanta da bukatunta?, don haka a karshe ina mai kara tunatar da mu cewa idan za ku so mutum ku so shi don Allah, haka ma idan za ku ki shi ku ki shi domin Allah. Allah kasa mu dace amin.
Sunana Ibrahim Umar Biraji, Malam Madori A Jihar Jigawa:
Eh! tabbas irin hakan yana yawan faruwa, dan zan iya cewa a yanzu wannan abun ma kamar ya zama ruwan dare, saboda mafi yawan ‘yan mata yanzu ba sa iya boye soyayyar su akan duk wanda suka ji a ransu ya burge su kuma suna son su kulla soyayya da shi. Tabbas a yadda na fuskanci ‘ya mace indai har ba wai tana jin shaukin so a kan ka mai karfin gaske ba, zai wahala ka samu ko da damar yi mata magane tana amsawa. Eh! kamar kuma wai kawo maka bukatunta don magance mata su, wannan shi yafi komai sauki, don sai mace ta yarda da kai ne za ta bukaci wani abu daga gareka. Sai dai idan kalar ballagazayen ‘yan matan da suka maida hakan tamkar sana’a. Eh! amma zai wahala mace ta takura maka sai kun kulla alaka da ita, kuma lokaci guda ta fara kawo maka wasu bukatunta don ka biya mata su, sai ta tabbatar da cewar eh lallai kai ma ra’ayinka ya karkata gareta za ta fara shigo da irin wannan abun din. To ka ga kuwa abun da kamar wuya kai ka ki aminta da hakan din sai dai har in baka da hanyar da za ka taimaka mata don biya mata bukatunta din. Kuma indai har soyayyar ta gaskiya ce kuma ana sanya rai akan cewar za ta iya zuwa har ga matakin Aure ai bana tunanin hakan zai iya zamtowa laifi, kawai sai dai shi saurayin ya yi hakuri, domin su daman mata dukkaninsu ‘yan hakuri ne. Idan baka da shi to zamantakewa da su zai mutukar yi maka wahala. Shawara ta a nan ita ce; ‘Yan mata su rika hakuri, da halin da muke a ciki yanzu, domin ba fa kowanne saurayi ne, za ki zo masa da tayin soyayya kuma ya karba da zuciya daya ba, ballantana har kina yunkurin kawo masa wasu bukatunki na yau da gobe da zummar wai ya biya miki su. Ni ina ganin kamar hakan kuskure ne, ita ‘ya mace ai da kunya aka santa, kuma ita ce ado mafi tsada a gurinta. Dan haka ‘Yan mata mu ji tsoron zamani, kada mu rika biyewa son duciyar mu. A koyi yaki da zuciya a kan lamuran yau da gobe, Ubangiji Allah ya kara tsarkake mana kirazan mu baki daya.