Kamfanin Dangote na Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN), wanda ke kera wa da tallata motocin Peugeot a Nijeriya, ya fara tarawa da haɗa sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna.
Peugeot 3008 GT, mai injin 1.6-lita turbo mai ƙarfi, ya ƙara yawan jerin motocin da ake haɗawa a masana’antar DPAN, wanda ya ya ke samar da 301 sedan da Peugeot 5008 mai kujeru bakwai. Wannan sabon samfurin yana da Faisal kamar fitilun, da hasken rana mai iya buɗewa, da tayoyin 17-inch alloy.
- Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu
- Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna
Hakanan, an samar da fasahar ABS don hana birki shanye wa, ESP don hana zamewa, da EBFD don daidaita birki bisa nauyin mota.
Motar na kuma ɗauke da fasahar Peugeot I-Cockpit, wacce ke da allon 12.3-inch mai nuna bayanai, touchscreen mai girman 8-inch, da kuma madannin tuƙi mai ayyuka da dama. Wannan ci gaba yana tabbatar da cewa DPAN na ci gaba da samar da motocin zamani masu inganci ga kasuwar Nijeriya.