Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ta shirya gudanar da bikin yaye ɗalibai karo na 39 daga Laraba, 12 ga Fabrairu, zuwa Asabar, 15 ga Fabrairu, 2025 inda dubban ɗalibai za su karɓi takardun shaidar kammala karatu, tare da bayar da digirin girmamawa.
Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa a ranar farko, ɗalibai 4,404 za su karɓi takardun shaidar kammala karatu na digiri da difloma.
- Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa
- Binciken Jami’ar Bayero Ya Gano A Hoton Yatsa Za A Iya Gane Mai Cutar Daji – Farfesa Darma
A rana ta biyu kuma za a yaye wasu ɗalibai 4,367 daga sassa bakwai na jami’ar, ciki har da 176 masu shaidar Digirin daraja ta Farko (First Class), da 2,590 masu digiri na biyu da kuma 275 masu digirin digirgir (Ph.d), sai kuma 535 masu Diflomar gaba da digiri Digiri (Postgraduate Diploma).
Kazalika za a gabatar da lakcar yaye ɗalibai, wacce Khalil Sulaiman Halilu, Mataimakin Shugaban NASENI, zai gabatar da kuma Ministan Kimiyya da Fasaha da Ƙirkire-Ƙirkire, Chief Uche Jeoffrey Nnaji, wanda shi ne zai shugabanci taron, inda jigon lackcar shi ne: “Ƙirkire-Ƙirkire da Kasuwanci: Hanyar Samar da ci gaban ƙasa.”
A ranar ƙarshe na bikin jami’ar za ta karrama wasu fitattun mutane da Digirin Girmamawa, ga Colonel Sani Bello, mai ritaya da Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, duba gagarumar gudunmawar da suka bayar ga al’umma, haka kuma za a naɗa Farfesa Garba Dahuwa Azare, da Farfesa Julius Afolabi Falola, da Farfesa Musa Mohammed Borodo da matsayin Farfesoshi Masu Darajar (Emeritus) saboda gudunmawarsu a fagen ilimi.