Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jaba/Zangon Kataf a Jihar Kaduna, Hon. Amos Gwamna Magaji, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Magaji ya sanar da sauya shekarsa ne a wata wasiƙa da kakakin Majalisa, Abbas Tajudeen, ya karanta a zaman majalisa na ranar Talata. Ya danganta ficewarsa da rikicin cikin gida da ke addabar PDP daga matakin ƙasa har zuwa jihohi.
- Gobara Ta Yi Sanadiyar Asarar Miliyoyin Dukiya A Kasuwar Katako Da Ke Jos
- Haƙar Ma’adanai Na Sa Yara Ficewa Daga Makaranta A Jos
Sauya shekar Magaji ya kara yawan ‘yan majalisar PDP da suka koma APC a majalisar wakilai ta 10 zuwa huɗu, bayan Hon. Chris Nkwonta (Abia), Hon. Eriatheke Ibori-Suenu (Delta), da Hon. Suleiman Gumi (Zamfara).
Sai dai jagoran marasa rinjaye, Kingsley Chinda (PDP, Rivers), ya buƙaci a ayyana kujerar Magaji a matsayin babu kowa, yana mai cewa bai bi tanadin doka kamar yadda Sashe na 68(1g) na kundin tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara) ya tanada ba.