Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024.
Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon albashin, an bar malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi a baya. Sun ce sun ba shugabannin isasshen lokaci domin su cika alƙawarin da suka ɗauka amma sun kasa, don haka suka yanke shawarar ci gaba da yajin aiki har sai an biya su hakkokinsu.
- Yadda Jami’an Tsaro Suka Fara Gyara Wa ‘Yan Jari Bola Zama A Abuja…
- Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje
A sakamakon yajin aikin, an rufe makarantu a sassa daban-daban na FCT, inda malamai suka sallami ɗalibai. Wata malama, Mrs. Ene Igado, ta ce malaman firamare na L.E.A ana yi musu babbar wariya idan aka kwatanta da takwarorinsu na UBEB, duk da cewa su ne ke yin mafi yawan aiki.