Kwamitin Rijista da Kula da cibiyoyin kiwon Lafiya Masu Zaman Kansu (PHERMC) ya rufe wata cibiyar lafiya mara rijista, mai sun “Dada’s Clinic & Maternity”, da ke Kapwa, a unguwar Gaube a cikin karamar hukumar Kuje ta Babban Birnin Tarayya (FCT).
Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a ga ministan babban birnin tarayya, Lere Olayinka, ya ce ma’aikacin asibitin mai suna Mista Sabiu shi ma an kama shi, kuma an kai shi ofishin ‘yansanda na Kuje.
- Da Ɗumi-ɗumi: Kotu Ta Dakatar Da Ohinoyi Na Masarautar Ebira
- Ƴansanda Sun Daka Wasoso Kan Gungun Ƴan Daba A Kano
Olayinka ya ce, a ranar 2 ga Fabrairu, 2025 da misalin karfe 3:32 na rana, wata tawaga karkashin jagorancin daraktan sashen kula da lafiya da bincike ne suka gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Asibitin.
“An zargi Asibitin da yin aiki ba tare da rajista ba da kuma yin ayyukan likitanci a cikin wani gidan haya da ake ganin bai dace da ayyukan kiwon lafiya ba.
“Bincike na farko ya nuna cewa, wani dattijo kuma shugaban Al’umma ya rasu sakamakon tiyata da aka yi masa a Asibitin, yayin da wasu rahotanni suka nuna cewa, majinyata da dama sun tsira da kyar daga bisani aka kai su wasu Asibitoci don samun kulawar gaggawa.
“Da isar su, tawagar binciken ta gano asibitin a cikin wani mawuyacin hali da rashin tsafta,” in ji shi.