Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar da yake yi a Birtaniya.
Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce ziyarar ta Wang Yi ta cimma nasara da kyawawan sakamako. Ya ce wannan shi ne karon farko da ministan harkokin wajen Sin ya ziyarci Birtaniya cikin shekaru 10, kuma karon farko da Sin da Birtaniya suka gudanar da muhimmiyar tattaunawa cikin shekaru 7, lamarin dake nuna kudurin bangarorin biyu na ci gaba ingantawa da daidaita dangantakarsu.
- 2027: Ganawar Kwankwaso Da Aregbesola Ta Haifar Da Cece-kuce A Fagen Siyasar Nijeriya
- Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Rufe Gasawar Wasannin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9
Yayin taron, Sin da Birtaniya sun yi tattaunawa mai zurfi kan yanayin duniya da batutuwa masu daukar hankali da ma tsarin tafiyar da harkokin duniya, tare da cimma matsaya mai muhimmanci.
Bangarorin biyu sun bayyana niyyarsu ta tattaunawa cikin gaskiya bisa mutunta juna da kuma hakuri da bambance-bambancen da sabanin dake akwai a tsakaninsu. Har ila yau, sun amince cewa Sin da Birtaniya za su karfafa tuntubar juna da hada hannu wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)