Gwamnatin Jihar Kebbi, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta samar da tirela 300 na abinci don raba wa ga jama’ar jihar a lokacin azumin watan Ramadan a faɗin ƙananan hukumomin 21 na jihar.
Bayanin hakan yans ƙunshe ne a cikin jawabin Gwamna Nasir Idris yayin da ya ke gabatar da jawabinsa na kammala ziyarar godiya a ƙaramar hukumar Mulki ta Birnin Kebbi da ya kai a ƙananan hukumomi 20 kafin kammala wa a Birnin Kebbi.
- Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Roma Da FC Porto
- Gwamnati Na ɗaukar Matakai Don Rage Farashin Abinci Ta Hanyar Zuba Jari A Noma – Minista
Gwamnan ya ce” A Matsayinsa na Gwamnan jihar ya zama wajibi gwamnatinsa ta samar da abinci ga al’ummar jihar domin su ne suka zaɓe ta . Haka kuma yana daya daga cikin alkawalin da ya dauka a lokacin yaƙin neman zabe a dukkan faɗin ƙananan hukumomin 21 na jihar cewa za a samar da walwala da jinda daɗi ga jama’ar jihar” Inji shi.
Bisa ga hakan, ya ƙara da cewa insha Allah satin farko na Azumi za a soma rabon abincin ga dukkan ƙananan hukumomi 21 na jihar da kuma sauransu. Gwamnan dai ya kara gode wa al’ummar jihar kan irin yadda suka sadaukar da kansu wajen bashi goyon baya. Ya ƙara ba da tabbacin sake samar da walwala da jin daɗi ga al’ummar jihar da kuma cigaba da samar da ayyukan da zasu sauya rayuwar al’ummar jihar Kebbi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp