A kwanakin baya, kasar Amurka ta gabatar da wata takardar bayani game da manufofin zuba jari, inda ta yi amfani da dalilin kiyaye tsaron kasa, da maida kasar Sin a matsayin kasar waje abokiyar gaba, da daukar matakan nuna bambanci ga kasar Sin a fannoni daban daban, da kuma kara kayyade zuba jari ga kasar Sin da kuma sa ‘yan kasuwan kasar Sin wani tarnaki wajen zuba jari a Amurka.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin 24 ga wannan wata cewa, Sin ta ki amincewa da wannan mataki, da tuntubar Amurka kan wannan batu. Kana kasar Sin za ta dauki matakai masu dacewa don tabbatar da moriyarta bisa doka.
- Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya
- Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje
Lin Jian ya bayyana cewa, Amurka ta kara yin bincike ga kamfanonin Sin da za su zuba jari a kasarta, inda batun ya karya lagon imanin kamfanonin Sin wajen zuba jari a Amurkar da kuma yanayin ciniki a kasar.
Kara kayyade kamfanonin Amurka masu zuba jari a kasar Sin ita ce manufar da aka gabatar wajen tsoma baki kan harkokin kamfanonin kasar ta Amurka, wadda za ta kawo illa ga hada-hadar zuba jari a tsakanin kasashen biyu.
Kasar Sin ta kalubalanci Amurka da ta bi ka’idojin zuba jari da tsarin gudanar da ciniki na kasa da kasa, da dokokin tattalin arzikin kasuwanci, da dakatar da siyasantar da batun tattalin arziki da cinikayya ko maida batun a matsayin makami, da kuma dakatar da kawo illa ga ikon samun ci gaba na kasar Sin. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp