A ƙoƙarin aiwatar da shirin Renewed Hope Initiative na matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, uwargidan Gwamnan Kebbi, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, ta rarraba kayan noma da kuɗaɗen ga mata manoma 100 a masarautar Zuru.
Matan da suka ci gajiyar tallafin sun fito daga ƙananan hukumomin Zuru, da Fakai, da Sakaba da Danko-Wasagu, inda kowacce mace ta samu iri na shinkafa da masara, takin zamani da kuma Naira 50,000. Ta bayyana cewa shirin na da nufin bunƙasa samar da abinci da inganta tattalin arziƙin mata, tare da ƙarfafa su su zama masu dogaro da kai.
- Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
- Gwamnatin Kebbi Ta Samar Da Tirela 300 Na Abinci Don Rabo Da Azumi
A yayin raba tallafin, Hajiya Zainab ta ja hankalin matan da su tabbatar da amfani da kayan da aka ba su domin su samu riba daga noman da za su yi. Ta gargaɗe su da su guji sayar da kayayyakin noma ko ƙin yin amfani da su, inda ta ce duk wadda aka samu da irin wannan hali za ta fuskanci hukunci.
Ta ƙara da cewa gwamnatin jihar na da burin ganin mata sun taka rawa sosai a ɓangaren noma, domin hakan zai taimaka wajen tabbatar da wadatar abinci da kuma ci gaban tattalin arziƙin jihar.
A nata bangaren, Shugabar ƙungiyar mata manoma ta jihar, Hajiya Hadiza Kola, ta gode wa matar gwamna bisa wannan tallafi, tare da bayyana cewa akwai gasa da za a gudanar domin bai wa matan da suka fi ƙoƙari lada. Ta yabawa Sanata Oluremi Tinubu bisa ƙoƙarinta na tallafawa mata a faɗin Nijeriya, tare da alƙawarin cewa mata manoma a Kebbi za su yi amfani da damar da aka ba su don bunƙasa harkar noma a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp