Kungiyar da ke bibiya da bayar da bayanan alhazai ta ƙasa, ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da babban birnin tarayya Abuja da su gyara sansanonin alhazai na jihohinsu a ya yin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da jigilar alhazai ta shekara ta 2025.
A sanarwar da aka rabawa manema labarai a yau Laraba a babban birnin tarayya Abuja, shugaban kungiyar, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa sun dukufa wajen ganin an gyara sansanin alhazai na jihohi a sakamakon lalacewa da suka yi a yanzu.
- Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya
- NAHCON Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2025 zuwa 10 ga Fabrairu
“Kowa yasan maniyyata suna shafe kwana da kwanaki a sansanonin alhazai kafin su tashi zuwa ƙasa mai tsarki, amma mun samu bayanan cewa sansanonin su na bukatar gyara sosai”. In ji shugaban
Kungiyar ta yabawa gwamnonin jihohin Bauchi da Adamawa da Kaduna da Sokoto da babban birnin tarayya Abuja, a kokarinsu na gyara sansanonin maniyyatan.
Bugu da kari kungiyar ta yabawa gwamnatin jihar Osun bisa alƙawarin da ta yi, na gina katafaren sansanin alhazai na zamani wanda ake saran za a kammala kafin fara jigilar alhazan bana.
A karshe kungiyar ta bayyana cewa sansanonin za su samar da hanyoyin samun kuɗi, wanda hakan zai samar da kuɗin shiga ga jihohin da kuma walwalar maniyyata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp