• English
  • Business News
Saturday, October 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwa 5 Da Ke Sa Ido Fari Mai Ban Sha’awa

by Bilkisu Tijjani
3 years ago
in Ado Da Kwalliya
0
Abubuwa 5 Da Ke Sa Ido Fari Mai Ban Sha’awa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Masu bibiyarmu a wannan shafi na Ado Da Kwalliya barkan mu da warhaka, barka da sake haduwa a wannan makon.

Duk lokacin da aka yi zancen farin ido ko mai hade da jajajaja galibin ‘yan’uwa mata sukan yi sha’awar a ce suna da shi saboda alama ce ta koshin lafiya da kuma abin da ake son gani a wurin ‘ya mace.

  • Zabtare Dala Miliyan 418 A Bashin Paris Club: Gwamnoni Sun Mayar Wa Malami Martani
  • Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak

Yayin da ake kara girma, idanunmu kan sauya su ma, ba wai kawai wurin amfanin da suke mana ba har da yanayin kalarsu. Wasu za a ga idanunsu sun yi fatsi-fatsi, wasu rawaya-rawaya wasu kuma kan yi shudu-shudi.

Akan samu haka daga gado na iyaye da kakanni wasu kuma sanadin wani ciwo ne. A zahiri wasu ba su ba da kyawawan kulawa ga idanunsu, wasu kuma ba ma su yi kwata-kwata.

Idan idanu suna samun kyakkyawan kulawa, za a same su cikin koshin lafiya koyaushe. Abubuwa 5 da ke sa ido fari:

Labarai Masu Nasaba

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

  1. Kokwamba Wannan nau’in abinci an san shi da yawan ruwa a cikinsa, shi ya sa yake da karfi wajen taimaka wa gyara kalar ido ya zama fari. Har ila yau yana taimakawa wajen rage wani bakin kala da ake gani a ido musamman idan mutum ya gaji tibis. Idan kuna neman wani abu cikin sauki da ke sa ido fari, to ku rungumi amfani da kokwamba.
  2. Sanya wani abu mai sanyi a ido Amfani da wani abu mai sanyi a ido ba kawai yana taimakawa wajen kawar da kumburin ido ba ne, har ma yakan taimaka wajen mayar da ido ya zama fari. A rika tsoma tawul a ruwan sanyi ana matsawa a ido ko kuma a daura kankara a idon, za a sha mamaki. Idan aka rika matsa idon na tsawon minti 5 zuwa 10 na abin da aka sa mai sanyi na wasu lokuta a yini, ido zai yi fari abin sha’awa.
  3. Samun isasshen bacci na sa ido ya yi fari Samun isasshen bacci a kowane dare kamar na tsawon awa 7 zuwa 8 a kullum yana hutar da jijiyoyin idanu tare da dawo wa idon da kalar farin da yake da ita ta ainihi. Domin kara samun hutu yadda ya kamata da kuma mayar da farin ido, muna ba da shawara a rika wanka kafin a yi bacci.
  4. Amfani da ganyen shayi Ganyen shayi walau baki ko kore yana taka muhimmiyar rawa wajen sa hutu da kuma kara ingancin lafiyar ido. Idan ana amfani da ganyen shayi, idanu ba za su tsufa da wuri ba. Ganyen shayi na da matukar amfani wajen yaki da kwayoyin cututtuka da kuma abubuwan da ka iya sa idanu su yi ja.
  5. Yawaita shan kayan marmari da ganyayyaki Cin ganyayyaki na da matukar amfani wajen inganta lafiyar ido da kara masa fari. Haka nan shan kayan marmari.

Ko baya ga amfanin da kayan marmari da ganyayyaki ke yi ga ido, har ila yau sukan kuma taimaka wajen inganta lafiyar hanta da samun sinadarai masu amfani a jiki.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AdoFariIdoKulawaKwalliyaKyauMata
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sharhi: Siyasar Ubangida Da Zaben Shekarar 2023

Next Post

Tubabbun ‘Yan Ta’adda Sun Roki Yafiyar ‘Yan Nijeriya

Related

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

10 hours ago
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

1 week ago
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

1 month ago
Matsalar Al’ada Da Ciwon Mara Ga Mata
Ado Da Kwalliya

Matsalar Al’ada Da Ciwon Mara Ga Mata

1 month ago
Yadda Za A Magance Ciwon Sanyi (Infection) Da Tafarnuwa
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Ciwon Sanyi (Infection) Da Tafarnuwa

2 months ago
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
Ado Da Kwalliya

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

2 months ago
Next Post
Tubabbun ‘Yan Ta’adda Sun Roki Yafiyar ‘Yan Nijeriya

Tubabbun 'Yan Ta'adda Sun Roki Yafiyar 'Yan Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

October 4, 2025
Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 4, 2025
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

October 4, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

October 4, 2025
Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

October 4, 2025
Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

October 4, 2025
Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

October 4, 2025
Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno

Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.